MAHAKURCI MAWADACI: Bayan shekaru 35 da aure, Allah ya azurta wata mata da ‘da namiji

0

Wata mata mai suna Dorcas Osiebo ta kwana cikin kuka na farinciki bayan Allah ya zurta ta da namiji bayan shekaru 35 da suka yi da mijin ta suna nema.

” Ko a lokacin da likita ta ce mini ina da ciki ban yarda ba domin tun a 2006 na dai na yin jini haila.”

” Na yi aure tun a 1984. Tun daga wannan lokaci muka yi ta fama da miji na. Babu irin cocin da ba mu je ba. Yau ace wannan gobe ace wancan.

” Bayan haka dai da abin ya gagara sai muka koma na gargajiya. Yau a bamu wannan jiko gobe wancan. Haka dai nayi ta fama. Kai a wasu lokuttan ma wasu abubuwan da ake bani nake kwankwada har tsoro suka rika bani.

” Wasu fa sai na toshe hanci na saboda dan karan wari da suke da shi. Haka zan yi ta sha dai domin in samu haihuwa. Nifa har aiki fida an yi a ciki na domin ko kila kaba ce ta toshe mahaifa ta amma ba muyi nasara ba.

Dorcas tace tun bayan haka sai ta hakura. Mijinta ma ya kura kawai sannan kuma ma a 2006 ta daina jini kwata-kwata.

” Tun da naga al’ada ta tsaya min sai na san cewa shikenan kuma bani babu haihuwa. Kwasam a wannan shekara sai likita ta aunani ta ce wai ina da juna biyu. Dama can kuwa kafin gwajin na rika jin bana jin dadin abinci a baki na sannan kuma jikin na ma sai a hankali.

” Dukka saoina duk sun haihu da ya’ya sannan wasu har da jikoki. kannni na ma da suka yi aure a baya na duk sun haifi ‘yaya har da jikoki.

Dorcas tace da ita da mijin ta suna cikin farinciki matuka a yanzu.

Share.

game da Author