Kakakin fadar shugaban Kasa Garba Shehu ya yi kira da babban murya ga wadanda ke sukan makusantar Buhari cewa wai suna tare da Buhari ne don su azurta kan su cewa wannan zato nasu ba gaskiya ba ne.
Garba Shehu ya ce dukka wadanda ake gani wai sune suka fi kusa da Buhari ‘ Abba Kyari, Mamman Daura da Samaila Isa Funtua’ attajirai ne masu abin hannun su ba tun yanzu ba.
” Babu talaka a cikin su. Dukkan su attajirai ne masu abin hannun su. Ina so kowa ya sani cewa dukkan su sun amfani kasa Najeriya kuma suna tare da Buhari ne domin su rika bashi shawarwari domin ci gaban Najeriya.
” Ya kamata mutane su daina cewa wai suna tare da Buhari ne domin su azurta kansu. Hakan ba daidai bane.”
Idan ba a manta ba, hatta uwargidan shugaban Kasa Aisha Buhari ta rika fitowa a lokutta da yawa ta na sukar makusantan Buhari musamman dan uwansa Mamman Daura. Cewa sune suke juya shi yadda suke so.
Garba Shehu ya kara da cewa babu wanda ya ke juya Buhari kamar yadda ‘yan Najeriya suke fadi.
” Babu wani makusancin Buhari da yake juya shi. Wadanda ke tare da shi duk mutanen kirki ne kuma mashahuran attajirai ne da kasa ta amfana da su a baya. Suna tare da Buhari ne domin su rika bashi shawara domin mulkin sa ta yi kyau sannan don a samu ci gaba a kasa.
Garba shehu ya bayyana wadannan kalamai ne a hira da yayi da Talabijin din Channels ranar Kirsimeti.