HATTARA DAI BUHARI: Kasafin 2020 Dankare Yake Da Gidoga Da Harkallar Naira Bilyan 264

0

A lokacin da Shugaban Kwamitin Kula da Kasafin Kudade, Barau Jibrin ke damka Kasafin 2020 wanda suka amince da shi, ya bayyana hujjar kara wa kasafin wasu makudan kudaden da ya kira ‘‘kudaden da za su kara cike rarar kasafin da za a samu.”

Shi dai Shugaba Buhari tun farko naira tiriliyan 10.33 ya damka wa Majalisar Dattawa a matsayin ta kasafin 2020. Cif da cif dai naira tiriliyan 10,594,62,364,830 ne Buhari ya nemi amincewar majalisa a matsayin kasafin kudade.

Yunkurin Nunke Buhari Baibai

Yayin da Buhari zai saka wa kasafin 2020 hannu a cikin wannan makon, ya kamata Shugaban Kasa ya lura fa cewa Majalisa ta cusa kasafin ayyuka da dama a cikin kasafin, wadanda duk ayyuka ne da harkalla, barankyankyama da azuraren da suka gina bututun da kudade za su rika kwarara a ciki, su kuma kwashe bayan sun zurare.

PREMIUM TIMES ta samu bin diddigin kasafin ayyukan da Majalisa ta cusa a cikinnkasafin kudi, har na naira bilyan 264. Wadannan alkaluma da ayyuka Jibrin ya nemi yak are, duk bige ce kawai ’yan majalisar suka shirya.

’Yan Majalisa Ko ’Yan Gidoga?

Ita dai wannan hukuma a karkashin Ma’aikatar Cinikayyya da Zuba Jari ta ke. An labta kusan naira bilyan uku a cikin kasafin SMEDAN, wanda aka maida naira bilyan 14.85 daga bilyan 11.02.

’Yan Majalisa ne suka zurara wadannan kudade, da sunan cewa za a wasu ayyuka a wasu wurare da suka hada da gyaran hanyoyi, gina magudanan ruwa, da kananan hanyoyi.

Haka nan kuma an shirya gidogar maida kasafin Hukumar Kula da Kan Iyakoki ta Kasa, daga naira bilyan 3.73 zuwa naira bilyan 5.46.

Wannan hukuma mai suna ‘Border Communities Development Agency’, ta na karkashin Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ne.

Dama kuma tuni wani rahoto da ICPC ta fitar a cikin rahoton ta na Bin Diddigin Ayyuka, CPTG ta bi diddigin wurare 424 da aka yi ikirarin cewa an yi ayyukan kai wa al’umma dauki tsakanin 2015 zuwa 2018.

Rahoton ya nuna cewa Hukumar Inganta Al’ummar Kan Iyakoki da SMEDAN sun zama wani bututun da ake kwarara wa bilyoyin kudade, daga baya ana kwashewa a tsanake.”

An gudanar da wannan bincike ne a jihohi 12 da Babban Birnin Tarayya, Abuja a cikin 2019.

Ba A Tsinana Wa Mutanen Karkara Komai Ba Cikin Shekaru 10 – Buhari

Idan ba a manta ba, a cikin watan Nuwamba na wannan shekara, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa daga cikin naira tiriliyan 1 da aka ware cikin shekaru goma a cikin kasafin kudi, domin a yi wa jama’ar karkara aiki, an kashe kudaden, amma ba a tsinana wa al’ummar karkara komai.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke kaddamar da wani aiki a cikin watan Nuwamba.

Ba Tausayi Ba Tsoron Allah

Duk da cewa ‘yan majalisa na sane da kyau cewa babu kudi a Najeriya, tilas sai Najeriya ta ciwo bashi sannan za a iya yin wadannan ayyukan, wannan bai sa su nuna jin tausayi ko tsoron Allah su yi kaffa-kaffa daga shirya gidoga da harkalla cusa makudan kudade da sunan ayyukan raya karkara ba.

Gidoga Da Harkalla A Ofishin Mai Taimaka Wa Buhari A Shirin Muradin Karni (MDGs)
Babu inda aka shirya gidoga kiri-riki da rana tsaka kamar ofishin Mai Taimakawa Ga Shugaban Kasa a Bangaren Muradin Karni, wato Millenium Development Goals (MDG) a takaice.

Ofishi ne da ke karkashin Ofishin Shugaba Buhari, kuma kasafin kudin da Buhari ya ware masa, gaba naira milyan 34,006,614.

Amma a sabuwar kwaskwarimar da Majalisa ta yi wa kasafin, sai ga shi sun cusa aikin naira bilyan 5.106. Watau an yi karin naira bilyan 5.072.

Abin da ke faruwa a irin wadannan wurare shi ne, su ‘yan majalisa ne za su tura kamfanonin da za a ce za a bai wa kwangiloli, sai a yi raba-biyu, kowa ya yagi ranon sa. Ko kuma gaba daga a kwashe kudaden ba tare da an yi aikin ba.

Ire-iren wadannan gidoga, ba za ka taba ganin wani aikin da za a je a ga an gina wani katafaren ayyukan inganta jama’a ba.

Sai dai ka ji wata irin gidoga, ko dai ka ji “an kai kaya ko takin shinkafa a Katsina, ko masara ko wake”, ko kuma ka ji “kudin samar da Keke NAPEP da babura, keken dinky ko motoci a Katsina”, da sauran su.

Yadda Aka Makanta Ilmin Firamare da Tsinin Biro

Fannin Ilmin Bai Dayan a Universal Basic Education da aka shirya wa kasafin naira bilyan 4.605, sai ga shi an lafta karin naira bilyan 25 a ciki, an maida shi zuwa bilyan 26.179.

Da haka da haka ake shirya gidoga da harkallar kudade, wadanda idan aka bi diddigi a karshen shekara, sai dai a gan su a rubuce, amma a neme su a aikace a rasa.

Don haka Shugaba Buhari sai a yi hattara. Kasafin Kudin 2020 da aika a majalisa, an yi masa irin yadda aka saba yi wa kasafin kudi shekara da shekaru. Babu wani canji da aka samu. Wato APC da PDP duk Danjuma ne da Danjummai, wadanda Jummai da Danjuma suka haifa.

Mu na dauke da sauran badakalar da Majalisa ta shirya a cikin Kasafin Kudin 2020.

Share.

game da Author