Babu gaskiya a Kalaman Alfindiki, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Fa’izu Alfindiki, tabbas naga rubutun ka, wanda yake cike da shirme, soki-burutsu da jahilci karara a ciki. Toh amma abun da baka sani ba shine, ita farfaganda ba haka ake yin ta ba, da ilimi ake yin ta, ba da sharri, kazafi da karya ake yi ba.

Alfindiki, ka zo kana ta ihun banza, kana karya, kana yadawa a Facebook da sauran kafafen yada labarai na zamani, kana cewa wai Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, adalin Sarki, ya tafi wurin taron yaye dalibai na Jami’ar North West, amma ya gudu saboda zuwan “Sarakunan Gaya, Bichi, Karaye da Rano.”

Ka ji shirmen banza da karya, jahili kawai, shashasha. Bayan su kan su masu bibiyar ka sun gane cewa kai makaryaci ne, domin Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagoranci wanda kuke yiwa karen farauta, kuna cin mutuncin shugabanni masu mutunci, wato Ganduje, ta daina gayyatar Mai Martaba Sarki wurin tarurukanta, ba domin komai ba, sai saboda irin muguwar nifakarta!

Kai Alfindiki, karen farautar ‘yan siyasa, wanda ya mayar da rigimar Masarautar Kano mai daraja da gwamnatin jihar Kano hanyar cin abinci. Yanzu tambayoyin da zan yi maka, kuma nike bukatar amsar su cikin gaugawa su ne:

Na farko: Don Allah wace irin mota Mai Martaba Sarki ya hau, da irin kayan da yasa, tun da ka iya bayar da labarin karya, irin wadda ka koya a gidan ku?

Na biyu: Shin wace irin firgicewa ce Mai Martaba Sarki zai yi don ya hadu da wasu “Sarakunan” da ko kusa basu kai shi matsayi ba?

Na uku: Ya kai Algungumi, afwan, Alfindiki, da kake maganar cewa wai Mai Martaba ya sauka yana fushi, shin biyo shi ka yi daga filin taron zuwa kofar kwaru din?

Na hudu: Ka san cewa yanzu muna zamani na kimiya da fasaha, wanda kowane irin motsi mutum yayi akan iya yi masa shigar bazata, ta yin amfani da na’urar wayar salula, a dauka a hoto.
Shin za ka iya nuna muna lokacin da Mai Martaba Sarki ya juya, tun da an yi abun ne cikin dubun-dubatar mutane ne ba a boye ba?

Alfindiki, shin ka manta da cewa, Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, shine mutumin da yayi gaba-da-gaba da tsohon shugaban kasar Najeriya, duk da yana karkashin sa, yana aiki a gwamnatin sa, a matsayin gwamnan babban banki kasa, ya fadi kuskuren sa, kuma yayi nasara a kan sa, wato Goodluck Ebele Jonathan? Yanzu don Allah wanda yake haka yaushe za ka yi tsammanin zai ji tsoron wani mutum da ba Allah ba, Sarki ne shi ko gwamna ne?

Kawai don Allah ya kawo mu wani zamani na rashin kunya, zamanin da ‘yan tasha suka yawaita, aka wayi gari ba sa ganin kima da Muhibbar Sarakuna, shine za ka zo kana ta shirmen ka da soki-burutsun ka, kuma wai kai Fa’izu Alfindiki, a haka suka yi maka mukamin saboda lalacewa?

Toh abun da baka sani ba shine, zan rantse maka har ga Allah, cewa kai ba ka ma tafi wurin taron ba. Domin ko gwamna ma bai tafi ba, mataimakin sa ne ya tafi. Kuma Mai Martaba Sarki babu wani taro da ya fita balle har yaje ya dawo gida. Kuma kai kanka ka san da cewa kowa ya gane ka, kuma kowa ya gama fahimtar ka cewa tuni daman ka tsani Mai Martaba Sarki, kuma kai makiyin sa ne. Shi yasa duk abun da za ka fada game da shi babu mai yarda, sai ‘yan gareji irin ka, domin an san karya ce kawai tsagwaron ta!

Daga karshe ina mai yi maka nasiha, kai da iyayen gidan ka, da kuji tsoron haduwar ku da Allah mahaliccin ku, domin akwai lokacin da zaku yi bayani dalla-dalla akan abun da kuka aikata ko kuka fada a cikin wannan duniya, a lokacin da babu gwamna Ganduje, kuma babu wata kujera sai ta Allah.

Ina kiran ku da kuyi hakuri da ikon Allah, domin farin jinin Mai Martaba Sarki ikon Allah ne. Ba yin sa bane yin Allah ne. Don haka wallahi duk wanda yace za ya ja da ikon Allah, toh na tabbata ba zai yi nasara ba, kuma karshen sa jin kunya da yardar Allah!

Kyautatawa talakawa da Mai Martaba Sarki yake yi, da iya mu’amalantar kowa da kowa ta hanya mai kyau, shi yasa suke son sa, kuma suke kaunar sa. Kullun mahassada suna yakar sa, amma har kullun kara farin jini yake yi.

Sun dauki hayar wasu gurbatattun malaman jami’ah, sun biya su makudan kudade, don suyi rubuce-rubuce, su bata sunan Mai Martaba Sarki, amma kullun suna yi amma Allah yana kara cusa kaunar sa a cikin zukatan al’ummah, ba domin komai ba sai don gaskiyar sa, ikhlasin sa, hakurin sa, son talakawan sa da tsoron Allah da yake da shi.

Saboda haka muna kira da su ji tsoron Allah, su sallamawa ikon Allah! Idan ba haka ba kuwa, wallahi karshen su nadama da dana-sani!

Daga karshe, ina rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala da yaci gaba da kare muna mutuncin Mai Martaba Sarki, amin.

Wassalamu Alaikum,

Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa ta wannan lamba kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author