LALACEWAR HANYOYIN NAJERIYA: Kamfanin Julius Berger sun yaudari gwamnati – Hadimin Buhari

0

Mai taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin Yankin Neja Delta, Ita Enang, ya bayyana cewa kamfanin gine-gine na Julius Berger ya yaudari gwamnati kan gyaran titin Calabar-Itu.

Ita Enang ya bayyana cewa kamfanin ya ki yin aiki kamar yadda yayi alkawarin zai yi a wannan Titi.

” Ganin cewa nan bada dadewa ba za a samu yawan mutane matafiya domin bukukuwan kirsimeti da na sabon shekara. Mun umarci Kamfanin Julius Berger ya gaggauta yin faci-faci a wasu wurare da suka yi matukar baci saboda matafiya su samu sauki.

” Amma abin mamaki da tashin hankali a kai shine da na isa wurin da aka bada aikin babu abin azo a gani da kamfanin ya yi banda jan kasa aka lafta a kan titin.

Ita Enang ya ce da zarar ya komo garin Abuja zai yi maza-maza ya garzaya ma’aikatat ayyuka domin kai kukan sa.

Manyan titunan gwamnatin tarayya a kasar nan sun lalace matuka sannan har yanzu babu daya da za a ce gwamnati ta gina har an kaddamar da shi wannan titi tun dava 2015.

Idan ba a manta ba Ministan Ayyuka, Babatunde Fashola ya bayyana cewa titunan Najeriya ba su yi lalacewar da mutane ke ta korafi akai ba, cewa wai zumudin mutane ne amma ba irin lalalcewar da suke fadi ba.

Fadin haka ke da wuya kuwa sai wani dan majalisar Tarayya ya kalubalanci minista Fashola da ya zo su zagaya kasar nan kaf ya nuna masa wani hanya ko da daya ne da gwamnati ta yi tun bayan rantsar da itaa ko kuma ta gyara, ko kuma take da kyau kasar nan.

Share.

game da Author