Ko ka san cewa rashin yin amfani da makilin din da ya kamata na cutar da hakora?
A shafin sun na Twitter kungiyar likitocin hakora (NDA) sun yi kira ga mutane da su ringa amfani da makilin din dake dauke da yawan sinadarin ‘Fluoride’ din da ya kamata cewa rashin yin haka na cutar da hakora da bakin mutum.
Sinadarin ‘Fluoride’ sinadari ne dake tsaftace baki, kara karfin hakora da hana bakin mutum kamuwa da cututtuka.
Sai dai kuma likitocin sun yi gargaddin cewa amfani da sinadarin a yawan da bai kamata ba na cutar da baki da hakoran mutum.
Hakan na nufin cewa idan makilin din da ake wanke baki da shi da safe ko da dare na dauke da wannan sinadari kasa ko fiye da yawan da ya kamata mutum na tattare da kamuwa da matsaloli a hakokarnsa da bakinsa.
A dalilin haka likitocin ke kira ga mutane da su ringa duba yawan wannan sinadari dake cikin makilin din da za su siya domin gawamnatin tarayya ta amince masu sarrafa makilin su dinga zuba 950 -1500 Part Per Million (PPM)’ na fluoride a cikin makilin domin mutane su yi amfani da shi cewa wannan yawan ne kadai ba zai cutar da hakoran mutum ba.
Sun kuma yi kira ga iyaye da su daina bari ‘ya’yan su kanana na hadiyan makilin domin yin haka na cutar da kiwon lafiyar su.
“Sannan iyaye sun tabbatar ‘ya’yan su kanana na amfani da makilin din da aka sarrafa domin su saboda amfani da makilin din da manya ke amfani da shi wa yara kanana na cutar da hakoran su.
Idan likitan hakora ya tambaye ka irin makilin din da kake amfani da shi hakan na nufin cewa akwai alamun makilin din da kake amfani da shi na cutar da hakoran ka.