A dalilin rashin tsaro da ake fama da shi a jihar Zamfara da hubbansan da gwamnati take yi na ganin an kawo karshen haka, ta sanar da kwace duka filaye da gonakin da gwamnatocin baya suka raba wa mutane tyn daga 1999.
A sanarwar da kakakin gwamnatin jihar Zamfara Yusuf Idris, ya fitar, daga yau Asabar 30 ga watan Nuwamba, gwamnati ta kwace duka wani gona ko fili da gwamnati ta taba ba wani tun daga 1999 zuwa yanzu.
Sanarwar ta ce yadda aka raba wadannan gonakin sune ummul-aba-isan kawo rikice-rikice da rashin zaman lafiya da yaki ci yaki cinyewa a jihar.
” Yadda aka raba gonaki a baya shine ya kawo rashin jituwa a tsakanin musamman manoma da makiya a jihar. Hakan kuma shine ya sa aka rika samun tashin hankali a jihar.
Bayan haka gwamnati ta kafa kwamiti da zai sake duba yadda aka raba wadannan filaye sannan kuma ya raba su yadda ya kamata. Wannan aiki da aka ba wannan kwamiti ya fara ne nan take.
Gwamnatin Zamfara ta ce yin haka zai taimaka matuka wajen samar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin Fulani da makiyaya da kusan kullum suna cikin tashin hankali hare-hare.
Gwamna Bello Matawalle ya na samun yabo matuka daga gwnatin tarayya da mutanen jihar Zamfara bisa maida hankali da yayi wajen ganin an samu zaman lafiya na din-din-din a jihar da sannan yadda yake kawo ayyukan ci gaba a fadin jihar.