Fitacciyar mawakiyar Hausa kuma ‘yar wasar fina-finan Kannywood ta sha ruwan yabo da jinjina daga dubban masoyan ta a dalilin karramawa da ta samu a kasar Faransa.
A Makon da ya gabata ne aka karrama mawakiya Fati Nijar a Kasar Faransa.
An karrama Fati a da sarautar Gimbiyar Mawakan Hausa dake nahiyar Turai.
Wannan kasaitaccen biki dai ya auku ne a fadar sarkin Hausawan kasashen Nahiyar Turai Alh Sirajo Jan Kado a garin Paris kasar Faransa.
Baya ga Fati Najeriya, an nada wasu mata biyu Jakadiyar Sarki da Giwar Mata.
Daya daga cikin wadanda a ka nada shine hHakimin garin Landan dake kasar Birtaniya, Muhammadu Sanusi
Dubban masoyan mawaki Fati Nijar da abokan aikin ta sun yi tururuwa zuwa shafukanta na sada zumunta domin taya ta murnar wannan karramawa da aka yi mata.
” Allah ya kara daukaka, ya tayi ki riko. Muna miki fatan Alkhairi.”
” Muna taya ki murna.”
BBC Hausa da ta ruwaito cewa sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya ziyarci wannan fada a watan da ya gabata.
Sarki Siraj ya bayyana cewa ya kafa irin wannan masarauta ne a kasar Faransa domin ya nuna wa dubiya irin kyawawan al’adun Hausa da kuma hada kan Hausawan dake kasashen Turai.