Dalilin da ya sa majalisar mu ta ki amince wa Buhari ya ciwo bashin biliyoyin daloli – Sanata Shehu Sani

0

Tsohon Sanatan dake wakiltar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa majalisar da ta gabata ta ki amince wa Bubari ya ciwo bashin biliyoyin daloli shi don ta ceto Najeriya daga sarkakin bashi.

” Basukan da ake bin Najeriya a 2015 sun kai Dala biliyan 10.32. A yanzu kuwa ana bin Najeriya akalla Dala Biliyan 22.8. Da ace mun saka masa hannu da bashin mu na waje kawai ya kai dala biliyan 52.

” Abin da nake so kowa ya sani shine yadda gwamnatoci ke ciwo bashi a kasar nan, nan ba da dadewa zamu zama bayin dole sai yadda kasashen duniya suka yi da mu da ‘ya’yan mu.

” Za kuji ana ta cewa wai ai kasar Amurka ma da ta ci gaba ta na ciwo bashi. Shi kenan don wata kasa na karbar bashi, Najeriya ita ma sai ta rika tunkaho da haka tana ciwo wa.

” Idan muka ce za mu rika sauraren ‘yan kwangila ne da bankuna, to ko lallai za mu rika cin bashi a kasar nan. Daga baya mu bari wa ‘ya’yan mu basukan da zai wahalar da su ya maida su bayi.

Sanata Shehu Sani ya kara da cewa duk wadanda suke zuga gwamnati ta ciwo bashi, yan kwangila ne da maso son karbar kwamishan daga cikin kudaden da ‘yan harkalla kawai amma ba ma su son ci gaban kasa ba ne.

A karshe, Shehu Sani ya ce lallai cin wadannan basuka babu abinda zai yi wa kasa sai dai tara wa na baya dimbin basukan da zai cukuikuyesu, ya maida su bayin dole ga kasashen da aka ciwo wadannan basukan daga nan gaba.

Share.

game da Author