BINCIKE: Yawan mutanen dake ta’ammali da muggan kwayoyi a Najeriya ya fi yawan mutanen wasu kasashen Turai

0

Kungiyar masana kimiyyar hada magunguna na Najeriya (PCN) ya koka da yadda mutane musamman matasa ke hadiyar kwayoyi babu gaira babu dalili.

Rajistaran kungiyar Elisha Mohammed ya bayyana haka ne a taron tattauna hanyoyin da za a iya bi wajen kawar da wannan matsala a Najeriya da aka yi a jihar Kaduna.

Mohammed ya ce sakamakon binciken da ‘World Drug Report’ ya gudanar ya nuna cewa akalla mutane miliyan 14.4 ne ke ta’ammali da miyagun kwayoyi a kasar nan.

Binciken da aka gudanar a 2019 ya kara nuna cewa ‘yan shekara 15 zuwa 64 ne suka fi ta’ammali da miyagun kwayoyi a kasar nan.

Mohammed ya ce lokaci ya yi da Najeriya za ta mike tsaye sannan ta maida hankali wajen kawar da wannan matsala ganin cewa mafi yawan mutanen dake ta’ammali da kwaya mutane ne da idan suka gyaru za a samu ci gaba a kasa sosai.

Daga nan sai jami’ar PCN Oluwatoyin Odeku ta yi kira ga gwamnati da kara kaimi wajen yin gargadi ga matasa kan illolin dake tattare da shan miyagun kwayoyi.

Tsohon dan wasan kwallon kafar Najeriya Daniel Amokachi ya yi kira ga gwamnati da ta yi amfani da wasanni wajen karkatar da hankulan matasa yana mai cewa yin haka zai taimaka matuka wajen kare matasan daga fadawa cikin wannan matsala musamman wadanda ba su bi sahu ba.

Idan ba a manta ba a bisa sakamakon binciken cibiyar yaki da Ta’ammali da miyagun kwayoyi na majalisar dinkin duniya (UNODC), hukumar NBS, cibiyar (CRISA) da kungiyar EU ya nuna cewa akalla mutane miliyan 14.3 na ta’ammali da kwayoyi a Najeriya.

EU ta gabatar da sakamakon wannan bincike ne a Abuja inda ta kara da cewa adadin yawan mutanen dake Ta’ammali da Kwayoyi a kasar nan ya fi adadin yawan mutanen dake wasu kasashen turai.

Sakamakon ya kuma nuna cewa ‘yan shekaru 15 zuwa 64 ne suka fi fadawa cikin wannan matsala sannan a cikin mutane hudu dake fama da wannan matsalar daya mace ce.

Sannan kuma kwayoyin da amfani da su ya zama ruwan dare a kasar nan sun hada da hodar ibilis, tabar wiwi, kwayar tramadol da maganin tari kodin sannan kuma a Arewacin Najeriya ne abin yafi muni.

Share.

game da Author