Cikin watannin da suka gabata PREMIUM TIMES Hausa ta kawo labarin yadda manyan ‘yan siyasa a Jihar Jigawa ke kokarin danne shari’ar wasu da aka kama da laifin garkuwa da mutane.
Wadanda ake zargin dai duk ‘yan sanda sun damke su, bayan sun yi garkuwa da wata gyatuma mai suna Hajiya Lubabatu.
Sun arce da Lubabatu, a lokacin da suka dira gidan dan ta, Abdullahi Mohammed, inda ta ke zaune a ciki, suka yi gaba da ita. Bayan kwanaki uku, shi Abdullahi din ya biyar kudin fansar karbo mahaifiyar sa har naira milyan 5.
A yau kuma, PREMIUM TIMES ta kawo muku labarin yadda aka dira gidan aka yi garkuwa da ita, yadda ‘yan bindigar, wadanda mazauna karkarar Malam Madori da Kaugama ne a jihar Jigawa, suka karbi naira milyan 5 daga Abdullahi, dan Lubabatu.
Abin al’ajabin shi ne yadda suka nemi gafara bayan sun karbi kudi, a lokacin da su ke damka gyatumar a hannun Aliyu Mohammed, wanda ya je ya kai kudin fansar, ya maida ta gida.
Malama Lubabatu ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa cikin dare wajen 1:30 suka dira cikin gidan, inda suka daure maigadi, kuma umarci ya kai su dakin da ta ke da sauran mutanen gida.
Bayan maigadi ya tashe su, a karshe dai sun tafi da ita, bayan sun karbi kudi naira 48,500 a hannun ta. Amma ba su tafi da kowa daga sauran mutanen gidan ba.
Sunn rika kiran dan ta, kuma maigidan, Abdullahi Mohammed da lambar waya GSM No. 09054170931, wadda daga baya ‘yan sanda suka gano ta wani malamin makarantar firamare ce a Malam Madori, kuma shi ma da shi aka yi garkuwar, har aka raba kudin aka ba shi naira 500,000.00. Sunan malamin Ahmed Isa.
Bayan sun boye matar a dajin hanyar Gumel zuwa Malam Madori, sun umarci a kai muksu kudin fansa a can, kuma aka aiki wani dan uwan mai gidan, mai suna Aliyu ya je ya kai kudin.
Wanda ya je kai kudin da ita kan ta wacce aka yi garkuwa da ita, ta ce wadanda suka yi garkuwar da ita su na magana da Fulatanci ne da Hausa.
Adullahi da mahaifiyar su Lubabatu, sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa lokacin da aka je kai kudin, wanda ya fito domin ya karbi kudin ya buga waya a sansanin su cewa a kawo ta, domin ga kudi ya karba, kuma sun cika.
Ta ce nan da nan aka fita da ita daga cikin jeji, aka kai ta inda wanda ya je kai kudi ya ajiye mota. Sun tambaye ta ta san wanda ya je kai kudin. Lubabatu ta amsa musu cewa ta san shi. Su ka kara tambayar ta ko ta amince ya tafi da ita zuwa gida? Ta ce ta amince. Daga nan aka damka masa ita, ya maida ta gida.
Rashin kunya a wajen mai garkuwa da mutane, ta sa ya dubi Hajiya Lubabatu a lokacin da ya damka ta ga Aliyu wanda ya kai musu kudi, ya ce ma ta don Allah ta yafe musu, su ma ba da son ran su ne su ke aikata laifin garkuwa da mutane ba.
Bayan ‘yan sanda sun kamo wadanda suka yi garkuwar, kuma sun amsa laifin su. An rika walle-walle da shari’ar ta su a ofishin Antoni Janar na Jihar Jigawa, inda aka yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa ne ke neman kashe maganar.
Sai dai kuma a labarin da PREMIUM TIMES Hausa ta buga a watannin baya, Antoni Janar din ya ce ba haka ba ne, alkalai ne suka tafi hutu, shi ya sa ba a tura shari’ar ta su zuwa kotu ba.