Kungiyar likitocin hakora na Najeriya (NDA) sun bayyana cewa cikin haihuwa ga ‘ya mace baya haddasa cirewar hakora.
Shugabannin kungiyar sun bayyana cewa wannan magana ba haka yake ba tatsuniyar gizo da koki ne kawai.
Likitocin Kungiyar sun kara da cewa hakorar mace kan rika fadi ne idan dama ita kazamiya ce ba ta wanke bakinta da kuma kula da hakoranta sai su rube suna fita da kansu amma ba daukar cikin haihuwa ba.
Sai dai kuma likitocin sun ce idan mace na da ciki jikinta na canja wa kamar haka:
1. Laulayin ciki
Laulayin ciki kan fara bayyana ne a yayin da mace ta fara yin amai da safe kuma dama hakan na faruwa ne a dalilin canjin yanayin da jikinta zai shiga.
2. Kumburi da ciwon dasashi
Hakan na aukuwa ne idan ciki ya kai wata hudu zuwa shida inda shima kan hana mace mai ciki wanke hakoranta ko kuma cin abinci.
3. Bushewar baki
Likitoci sun yi kira ga duk mata masu ciki da su rika shan ruwa akai- akai domin gujewa fadawa wannan matsala.
4. Yawan shan zaki
Likitoci sun yi kira ga mata masu ciki da su rage yawan shan zaki cewa shan zaki na daga cikin abubuwan dake haddasa kwayoyin cutar Bacteria wanda ke iya sa bakin mace wari ko kuma lalata hakora.
A karshe likitocin sun yi kira ga mata masu ciki da su rika tsaftace jikinsu musamman bakunan su saboda gujewa kamuwa da cututtuka. Sannan su jure shan magungunan da ake basi a asibiti a lokacun da suke da ciki.
Discussion about this post