Ba za mu tsaida shirin tare matafiya su nuna katin shaida ba – Buratai

0

Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Janar Tukur Buratai, ya bayyana cewa duk da korafe-korafen da jama’a ke yi, sojoji ba za su dakatar da shirin da za su fara a yau ba.

Sojojin Najeriya dai za su fara tare manyan titinan kasar nan, su na neman ganin katin shaida daga matafiya da ke cikin motocin zirga-zirga.

Buratai ya sha wannan alwashin ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya a ranar Alhamis, karkashin jagorancin Shugaban Kwamitin Tsaro, Abdulrazak Namdaz.

Ya ce sun fito da shirin ne domin kokarin zakulo ‘yan Boko Haram da suka tsere da kuma gano wasu tantiran masu aikata laifuka daban-daban a kasar nan.

Babban Jami’in Soja U.S Mohammed wanda ya wakilci Buratai a Majalisar Tarayya, ya ce ba wai sojoji za su kafa wasu shingaye ne a kan titi su hana motoci wucewa ko haddasa cinkoso kamar yadda aka yi tunani ba.

Ya ce jama’a da duk matafiya ba ma za su iya ganin wani canji ba, domin ba fitowa sojoji za su rika yi ko’ina su na kafa shingayen hana motoci wucewa ba.

Ya ce wannan shiri ya samu karbuwa sosai a yankin Arewa maso Gabas, inda ‘yan Boko Haram suka yi kaka-gida.

“Don kawai an ji sojoji sun ce za su gudanar da tantancewar a fadin kasar nan, ai ba wani sabon abu ne za mu kawo ba. Za mu rika aiki ne da rahoton sirri da mu ke samu, inda za a je a yi bincike, idan ta kama a yi kame, a kama na kamawa idan ana zargin sa karara.

“Ba wasu sojoji ne za a sake kawowa a jibge ana tare mutane ba. Wato mu na da hakikanin rahoton zirga-zirgar ‘yan Boko Haram, su na ficewa zuwa wasu kasashe. Shi ya sa za mu yi kokarin dakile su.

Ranar Talata ne dai Majalisar Tarayya ta nemi a tsaida aikin, domin kara wa kai wani nauyin tsaro ne sojoji ke neman yi, sannan kuma aikin ‘yan sanda ne.

Share.

game da Author