Kotun daukaka kara dake zama a Kaduna ta tsige dan majalisan tarayya dake wakiltan Bebeji/Kiru, Jihar Kano Abdulmumini Jibrin.
Alkalin Kotun Adejoje Adepoju wadda shine ya yanke wannan hukunci ya bayyana cewa dalilin da yasa kotu ta tsige dan majalisar shine ganowa da akayi cewa takardun da aka shigar da sakamakon zaben wa wancan lokaci ba sune ya kamata ayi amfani da su ba. Sannan kuma duk an lalata na ainihin.
Maishari’a Adepoju ya ce a dalilin haka dile ya sole zaben kwata-kwata.
Ya umarci hukumar zabe da ta sake gudanar da zaben dan majalisar tarayya na wannan kananan hukumomi biyu.
Discussion about this post