INEC za ta kirkiro rumfunan zabe, ta yi gyara a mazabu

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa a cikin watanni hudun farkon shekarar 2020, za ta kara kirkiro wasu rumfunan zabe da kuma yi wa mazabu gyara a fadin kasar nan.

Kwamishinan Zabe na Tarayya, kuma Jami’in Wayar da Kan Jama’a, Festus Okoye ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke jawabi a taron da INEC ya yi tare da Kungiyoyin Rajin Kare Dimokradiyya da Sa-ido kan Zabe, a Abuja.

Okoye ya ce INEC za ta tuntubi dukkan bangarorin da ke da ruwa da tsaki domin jin ta bakin su dangane da karin rumfunan zaben da za a yi.

Ya ce akwai rumfunan zabe 119,973 da kuma wuraren zabe 57,073 a fadin kasar nan.

Sannan ya ce INEC za su hada kai da Majalisar Dattawa da kuma ofishin Antoni Janar na Najeriya domin samun maslahar yadda za a saisaita karin da kuma gyaran su shiga cikin doka.

Daga nan ya yi kira ga ‘yan Najeriya su bada amanna da ayyukan da hukumar za ta gudanar.

Okoye ya ce a zaben 2019, wadanda ba su gamsu ba sun rubuta korafe-kotafe har 807. “Ya zuwa ranar 25 Ga Oktoba, an janye korafe-korafe 190, yayin da aka yi watsi da 570. Sai kuma aka bada nasara ga mutane ‘yan takara 44 da suka yi korafi.

Ya ce amma har yanzu akwai batun korafi 4 da ba a kai ga yanke wa hukunci ba tukunna.

Dangane da zaben gwamna a jihohin Bayelsa da Kogi da za gudanar nan da makonni biyu masu zuwa, Okoye ya ce INEC ba za ta amince a tauye hakkin wani ko wasu ba da nufin a hana su zaben wanda ran su ke so.

Kuma ya yi gargadin cewa kada a kuntata ko musguna wa kowa. Sannan kuma ya yi kira ga jami’an zabe su kiyaye sosai wajen ayyukan zabe a ranar zabe da kuma lokacin kidaya da tattara kuri’u.

Har ila yau, INEC ta yi kira ga EFCC su sa ido wajen damke duk wani dan takara ko dan siyasar sa ke yawo ya na raba kudi ko sayen kuri’u a ranar zabe.

Share.

game da Author