Tsohon gwamnan jihar Imo sanata Rochas Okorocha ya bayyana cewa a na shi ganin ba datse iyakokin Najeriya bane mafita idan har ana so abunkasa tattalin arzikin kasa da samarwa matasa aikin yi.
” Idan kuka duba, iyakokin da aka datse guda nawa ne? Ina so ku sani akwai sama da iyakoki 3000 da ke zagaye da Najeriya tun daga kasashen Benin, Kamaru, Nijar, Togo, Ghana, chadi da Nijar. Dazukan Allah-ta’ala ne da za iya yankowa a shigo kasar nan ta ko-ina.
Okorocha ya kara da cewa duk da yana goyon bayan mai da hankali da aka yi wajen ganin an bunkasa musamman noman abinci a cikin gida Najeriya , hakan ba shine zai sa wai a kubuta daga wannan mastsala da ake fama da ba.
” Sai an sama wa matasa ayyukan yi ta hanyar kafa masana’antu da zasu samu aikin yi shine mafita a ganina. Tun daga Sokoto zuwa Kano, Legas, Owerri, Ogun da Ondo idan ka zazzagaya, duk inda ka ga hayaki na bulbulowa to kada ka dauka wai masana’anta ce. Hayakin girki ne fa kawai. Ko ana girka farfesu, ko gasa kifi ko kuma ana dafa hadaddiyar dafadukan shinkafa da wake.
Bayannan da ya ke magan game da rikice-rikicen da ya dabaibaye jam’iyyar APC, Okorocha ya ce idan ba sake lale aka yi ba tabbas APC da Buhari za ta tafi a 2023.
KARANTA: Buhari na sauka a 2023, APC ta gama yawo – Okorocha
Okorocha ya ce duk jam’iyyar da ke fama da rigingimun da suka dabaibaye ta, kuma shgabannin ta suka kasa warware su, sai ma wasu rikice-rikice su ke rurawa da kan su, to bai ma kamata a kira wannan jam’iyya ba, sai dai a kira ta jamhuru.
“Wadannan rigingimu da ke ta bijirowa cikin APC, su na nuna cewa jam’iyyar a kara-zube kawai ta ke, babu wata takamaimen akida.
“Domin idan har akwai wata kyakkwar akidar da kowane mamba ya amince da ita, to babu wani dalilin da zai sa rihingimu su rika kunno kai.
“Babban kalubalen mu shi ne ba mu da wata alkibla ko manufa ko akida a jam’iyyar mu. Kawai dai abin nan ne da ake cewa ‘taron-kwaram-da-hama’, haduwar gidigo da ‘yan gidoga a wuri daya kawai. An gwamutsu wuri daya an kafa jam’iyya.
Ya ce idan ba hanzari aka yi aka magance wadannan rigingimu da shugabannin APC ke haddasawa ba, to za a wayi gari a zaben 2023 a kwace mulki daga APC ya koma hannun wata jam’iyyar da ta fi ta karsashi.
Idan ba a manta ba a watan Satumba, Sanata Okorocha ya koka kan yadda jam’iyyar APC ta rika yi masa sari ka noke duk da itrin gudunmawar da ya ba jam’iyyar tun a 2015.
” Wai ace a yau nine abokin gaban jam’iyyar APC a kasar nan duk da irin bauta mata da nayi a kasar nan da irin tallata jam’iyyar a yankin Kudu Maso Gabas amma duk da haka shugabannin ta sun kafa mini kahon zuka sharrin yau daban da na gobe.
” A yankin Kudu Maso Gabas, har ce mini ake yi wai ni ‘Inyamirin Hausawa ne’ amma duk da haka cin mutuncin yau dabam da na gobe ake yi mini a APC yanzu.
” Ni dinnan ina daga cikin wadanda suka yi ruwa suka yi tsaki aka zabi Oshiomhole shugaban jam’iyyar APC. Amma wai har jam’iyyar ce ke bin gwamnan jihar Emeka Ehiodioha ya dawo jam’iyyar APC idan har zai iya ci mini mutunci, ya wulakantani.
” Wannan abu da APC ta ke yi min ya tada min da hankali kuma yana bani tsoro domin kuwa na ga kamar ba a ma neman a gyara sai batawa ake yi. Yanzu dai ban san matsayina ba game da dakatar dani dajam’iyyar tayi amma ina nazari kuma ina nan a APC har yanzu sai dai ga dukkan alamu komai zai iya canja wa nan gaba.