An rika kira na ‘Inyamirin Hausawa’ a kasar Igbo saboda APC amma yanzu nine abokin gaban Jam’iyyar – Okorocha

0

Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha ya bayyana takaicin sa ga yadda jam’iyyar APC ta maida shi abokin gaba karara duk da irin bauta mata da yayi tunda 2015.

” Wai ace a yau nine abokin gaban jam’iyyar APC a kasar nan duk da irin bauta mata da nayi a kasar nan da irin tallata jam’iyyar a yankin Kudu Maso Gabas amma duk da haka shugabannin ta sun kafa mini kahon zuka sharrin yau daban da na gobe.

” A yankin Kudu Maso Gabas, har ce mini ake yi wai ni ‘Inyamirin Hausawa ne’ amma duk da haka cin mutuncin yau dabam da na gobe ake yi mini a APC yanzu.

” Ni dinnan ina daga cikin wadanda suka yi ruwa suka yi tsaki aka zabi Oshiomhole shugaban jam’iyyar APC. Amma wai har jam’iyyar ce ke bin gwamnan jihar Emeka Ehiodioha ya dawo jam’iyyar APC idan har zai iya ci mini mutunci, ya wulakantani.

” Wannan abu da APC ta ke yi min ya tada min da hankali kuma yana bani tsoro domin kuwa na ga kamar ba a ma neman a gyara sai batawa ake yi. Yanzu dai ban san matsayina ba game da dakatar dani dajam’iyyar tayi amma ina nazari kuma ina nan a APC har yanzu sai dai ga dukkan alamu komai zai iya canja wa nan gaba.

Okorocha ya kara da cewa sanin kowa ne cewa yanzu Buhari ne ke rike da APC kuma shine karfin jam’iyyar. Idan ya kammala wa’adinsa a 2023 jam’iyyar za ta watse idan ba a sake lale ba.

” Kowa ya sani cewa Buhari ne karfin wannan jam’iyyar. Shine ya ke hada kan ‘ya’yan jam’iyyar amma idan ya kammala wa’adinsa ina tabbatar muku da cewa komai fa zai canja saboda babu hadin kai a jam’iyyar.

” A yanzu ace wai har an fara maganan waye zai zama kaza sannan daga wani yanki za a zabi kaza. Maimakon a maida hankali wajen ganin Buhari ya cika alkawuran da ya dauka wa mutanen kasarnan. Yanzu har an fara raba mukamai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.

Share.

game da Author