Buhari na sauka a 2023, APC ta gama yawo – Okorocha

0

Sanata Rochas Okorocha daga Shiyyar Imo ta Yamma, ya dora laifin matsalar da ta dabaibaye jam’iyyar APC a kan shygabannin jam’iyar.

Okorocha ya ce hakan da ke faruwa alamomi ne da ke nuna cewa da wahalar gaske jami’iyyar APC ta sake cin zabe a 2023.

Ya yi wannan kakkausan hasashen ne a Kano, lokacin da ya ke magana dangane da rikicin da ya tirnike tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da Shugaban Jam’iyyar PDP, Adams Oshiomhole.

Okorocha ya ce duk jam’iyyar da ke fama da rigingimun da suka dabaibaye ta, kuma shgabannin ta suka kasa warware su, sai ma wasu rikice-rikice su ke rurawa da kan su, to bai ma kamata a kira wannan jam’iyya ba, sai dai a kira ta jamhuru.

“Wadannan rigingimu da ke ta bijirowa cikin APC, su na nuna cewa jam’iyyar a kara-zube kawai ta ke, babu wata takamaimen akida.

“Domin idan har akwai wata kyakkwar akidar da kowane mamba ya amince da ita, to babu wani dalilin da zai sa rihingimu su rika kunno kai.

“Babban kalubalen mu shi ne ba mu da wata alkibla ko manufa ko akida a jam’iyyar mu. Kawai dai abin nan ne da ake cewa ‘taron-kwaram-da-hama’, haduwar gidigo da ‘yan gidoga a wuri daya kawai. An gwamutsu wuri daya an kafa jam’iyya.

Ya ce idan ba hanzari aka yi aka magance wadannan rigingimu da shugabannin APC ke haddasawa ba, to za a wayi gari a zaben 2023 a kwace mulki daga APC ya koma hannun wata jam’iyyar da ta fi ta karsashi.

KARANTA: An rika kira na ‘Inyamirin Hausawa’ a kasar Igbo saboda APC amma yanzu nine abokin gaban Jam’iyyar

Idan ba a manta ba a watan Satumba, Sanata Okorocha ya koka kan yadda jam’iyyar APC ta rika yi masa sari ka noke duk da itrin gudunmawar da ya ba jam’iyyar tun a 2015.

” Wai ace a yau nine abokin gaban jam’iyyar APC a kasar nan duk da irin bauta mata da nayi a kasar nan da irin tallata jam’iyyar a yankin Kudu Maso Gabas amma duk da haka shugabannin ta sun kafa mini kahon zuka sharrin yau daban da na gobe.

” A yankin Kudu Maso Gabas, har ce mini ake yi wai ni ‘Inyamirin Hausawa ne’ amma duk da haka cin mutuncin yau dabam da na gobe ake yi mini a APC yanzu.

” Ni dinnan ina daga cikin wadanda suka yi ruwa suka yi tsaki aka zabi Oshiomhole shugaban jam’iyyar APC. Amma wai har jam’iyyar ce ke bin gwamnan jihar Emeka Ehiodioha ya dawo jam’iyyar APC idan har zai iya ci mini mutunci, ya wulakantani.

” Wannan abu da APC ta ke yi min ya tada min da hankali kuma yana bani tsoro domin kuwa na ga kamar ba a ma neman a gyara sai batawa ake yi. Yanzu dai ban san matsayina ba game da dakatar dani dajam’iyyar tayi amma ina nazari kuma ina nan a APC har yanzu sai dai ga dukkan alamu komai zai iya canja wa nan gaba.

Share.

game da Author