Tsohon Gwmnan Jihar Ogun Ibekunle Amosun wanda aka samu dumu-dumu cikin harkallar fasa-kwaurin muggan makamai a lokacin da ya ke mulki, ya yi takakkiya daga Najeriya har London a kasar Ingila, inda ya halarci shagalin murnar cikar Mamman Daura shekaru 80 da haihuwa.
An nuno Amosun a zaune kan tebur ya na ta zumudin taya Mamman Daura murna, a wani taron bikin da aka shirya wa Mamman Daura, wanda iyalan sa da ‘yan uwa da kuma masu uwa a gindin murhun Fadar Shugaban Kasa suka halarta.
Tsakanin Mamman Daura da Amosun dai babu dangin iya ko na baba da suka hada jini. Amma sai ga shi ya halarci shagalin bikin na dan uwan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kuma wanda ya fi kusanci da fada-a-ji a wajen Buhari.
An shirya wannan dabdala ce a daidai lokacin da Buhari ke hutun makonni biyu a Landan kuma a daidai lolkacin da labarin yadda gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa Amosun sumogal din makamai ya yi, ba a ba shi izni ba.
Cikin makon da ya gabata ne dai Gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa tsohon Gwamnan Jihar Ogun Ibekunle Amosun bai tsaya karbar izni ba ya yi sumogal din muggan makamai cikin Najeriya.
A cikin wata wasika da Darakta Janar na Kasafin Kudin Gwamnatin Tarayya, Ben Akabueze ya aiko wa PREMIUM TIMES kwanan nan, ya ce abin da Amosun ya nemi iznin sayo su ne motocin daukar jami’an ‘yan sanda 13 tun a cikin 2012.
Amosun ya yi gwamnan jihar Ogun daga 2011 zuwa 2019. Ya tsaya takarar sanata a APC a lokacin da ya ke daf da kammala wa’adin sa na gwamna, kuma ya yi nasara.
PREMIUM TIMES ta fallasa Amosun a cikin watan Yuni, inda ta fayyace yadda ya damka wa jami’an tsaro bindigogi 1,000 da harsasai milyan biyu da rigunan sulken hana harsashi huda mutum, ta tare da gabatar da shaidun cewa a bisa ka’ida ya shigo da makaman ba.
Jami’an tsaron da suka gulmata wa PREMIUM TIMES labarin yadda ya mika makaman, sun kara tabbatar da cewa akwai damuwa sosai idan aka bi diddigin yadda Amosun ya mallaki makaman masu tarin yawa, wadanda ya mika wa jami’an ‘yan sanda kwana daya kafin cikar wa’adin mulkin sa.
Wasu majiyoyin kuma sun kara cewa jami’an tsaro sun rika sa-ido sosai a kan Amosun a lokacin da zaben 2019 ya gabato, don kada ya zille ya yi amfani da wadannan muggan makamai wajen damka su ga ‘yan dabar siyasa.
Har yau kuma jami’an tsaro sun cika da mamakin yadda aka yi har Amosun a lokacin da ya ke gwamna ya iya yin sumogal din wadannan makamai masu yawa. Sannan kuma a na ta tunanin abin da ya yi niyyar yi da su da kuma hakikanin yawan su.
Wato su na tunanin watakila ma makaman da ya shigo da su din sun zarce yawan wadanda ya damka wa jami’an tsaro a ranar jajibirin da zai sauka daga mulki.
Da farko lokacinn da PREMIUM TIMES ta fara buga labarin, Amosun ya shiga shafin sa na Twitter ya karyata.
Daga baya kuma ya ce ya samu satifiket daga Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa a Fannin Tsaro, ya shigo da motocin daukar ‘yan sanda 13, bindigogi samfurin AK47 guda 1,000 da kuma harsasai milyan 2 a cikin 2012.
Amosun ya ce ya sayo makaman ne da nufin bai wa ‘yan sandan jihar sa gudummawar dakile aikata miyagun laifuka a jihar.
Ba wanda ya ba Amosun Izinin shigo da Makamai
A wasikar da Akabueze ya rubuto wa PREMIUM TIMES, ya bayyana cewa:
“Bayan na yi nazarin tambayoyin da ku ka bukaci amsa, to ina mai sanar da ku gaskiyar lamari cewa Sanata Ibekunle Amosun, tsohon gwamnan jihar Ogun ya nemi iznin shigo da motocin daukar ‘yan sanda guda 12.
“Ya aiko da wannan takardar neman izni a ranar 10 Ga Afrilu, 2012, kamar yadda wasikar sa mai lamba BO/R.10260/S.4/T.4/22 ta tabbatar
Wadannan motoci kamar yadda wasikar ta nuna, za a yi amfani da su ne wajen sintiri na hadin-guiwa tsakanin sojoji da ‘yan sanda a jihar Ogun.
Sai dai kuma Amosun ya ki bin shawarar Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Tsaro, inda ya wuce makadi da rawa, ya shigo da dimbin bindigogi da harsasai.
Jama’a da dama da masu rajin kare jama’a da m]kungiyoyi dai na ta rajin kiraye-kirayen a kama Amosun a hukunta shi.
KO BIRIS KO OHO
Duk da tafin Allah-tsine da aka rika yi wa Amosun da kuma kiraye-kirayen da masu kishin kasar nan suka rika yi cewa a kama shi a tuhume shi tare da hukunta shi, har yanzu babu abin da ya biyo baya.
Amosun ya tabka wannan aika-aika a lokacin da ya ke da kariyar sulke ta mukamin gwamna. Sai dai kuma an janye wannan garkuwar ko sulken tun ranar da wa’adin sa na gwamna ya cika, a ranar 29 Ga Mayu, 2019.
Ana mamakin yadda Amosun ke kara kutsa kai ya na neman samun shiga a gaban fadar shugaban kasa, ta hanyar cusa kai wajen sha’anin Mamman Daura, a daidai lokacin da aka fallasa harkallar fasa-kwaurin muggan makaman da ya yi.