Yadda Jami’o’in Najeriya ke bai wa daliban da suka fi saura bajinta kyautar kwandaloli

0

Jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu (COOU), ta bai wa Best Somadina kyautar mummuken doya daya, zakara da katin yabo, a lokacin da ya zama Gwarzon Dalibi Mafi Bajinta a Kwas din Aikin Jarida, cikin 2017.

“Mutane su yi tunanin za a ba ni kyautar wasu litattafi masu muhimmanci. Amma yayin da aka gan ni rungume da doya da zakara, sai aka rika gaggaba min dariya. Wasu ma sai suka ce ko dai na koma dan bori ko dan duba ko kuma dan tsibbu ne?

“Ni da a ce ma kwamfuta laptop suka ba ni ko wata naira 500,000 domin na zarce na yi digiri na biyu, ai da abin ya fi mutunci. Amma an ba ni zakara da doya. Sai ka ce na yi bajinta a kwas din rawar ‘yan bori.”

Bamisaye Tosin shi kuwa kyautar naira 200 kadagal aka ba shi a lokacin da ya zama Gwarzon Dalibi Mafi Hazaka da suka fita a Sashen Inginiya a Jami’ar Jihar Ekiti (EKSU). Tosin bai ji haushi ba. Karba ya yi ya soka abin sa aljihu.

Shi kuwa Oluwole da shi ma ke a Jami’ar Jihar Ekiti, tafiyar takama ya rika yi ya na tinkaho a lokacin da zai karbi kyautar Gwarzon Dalibi mafi bajinta a cikin daliban sashen su na nazarin kimiyyar kwamfuta.

A tunanin sa kyautar naira 100,000 ce aka rubuta masa. Sai da ya kara bude idanu ya ga lallai ashe naira 1,000 ce kacal. A nan take gaban masu mika masa kyautar ya bata ran sa.

Wani karin haushi, tun cikin 2017 wannan al’amari ya faru, amma har yau ba a damka masa kudin a hannun sa ba. Sai dai a rubuce kawai da aka rattaba aka ba shi.

Hikimat Ibrahim-Buruji kuwa duk da hikimar ta wajen yi wa sauran daliban Larabci da Nazarin Addinin Musulunci a Jami’ar Ibadan, a cikin 2016, naira 2,000 aka ba ta kyautar bajintar da ta yi.

Odewale Joseph na Jami’ar Ibadan ya taki sa’a ba kamar Hikimat ba, domin shi naira 25,000 aka ba shi a zarrar da ya yi da ya ke shi a digirin sa na biyu ne.

Masanin ilmi Mohammed Abba daga Gombe cewa ya yi ya kamata jami’o’i su rika saka wa daliban da suka yi bajin ta ta hanyar sama musu aikin yi, gurbin karo ilmi gaba da kuma kudade masu daraja.

“Za su iya hada karfi da manyan kamfanoni da cibiyoyin bayar da tattafi irin su Dangote domin bayar da kyaututtukan.”

Adaobi Abisi ya kasance wanda ya fi saura bajinta a kwas din digiri kan Aikin Banki da Hada-hadar Kudade. Ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ko kwandala ba a ba shi ba.

Fatimah Tafoki ta Jami’ar Abuja kuwa ta samu kyautar Naira 100,000 daga kamfanin Etisalat a shekarar farko a matsayin ta na mafi karancin shekaru kuma wadda ta yi bajin ta a fannin kimiyyar kwamfuta. Sai dai kuma a shekarar karshe da ta kammala digiri din kuma za yi zarra fiye da kowa, ba a ba ta kyautar ko sisi ba.

Cikin 2018, irin wannan abin takaici ya fusata Kungiyar Daliban Kwalejin Fasaha ta Lagos, inda suka rubuta wa gwamnan lokacin wasika cewa ba su ji dadin gaisawar da kawai ya yi da Easter Fatogun, dalibar da ta fi dukkan saura hazaka ba, ba tare da ba ta kyautar komai ba.

Share.

game da Author