Jami’an tsaro na SSS a jihar Kebbi sun damke wasu mutane hudu da dake Sace yaran mutane a jihar.
Da yake mika wasu yara da aka ceto daga hannun wadannan masu garkuwa ga iyayen su gwamnan jihar Atiku Bagudu ya bayyana cewa jami’an SSS sun kama Mrs Comfort Nwankow ma’aikaciyar asibitin koyarwa na jami’ar ‘Usaman Danfodiyo’,Uchenna Benedict,Helen Samuel, da wani Moses dake zama a Zuru.
Ya ce dubun wadannan mutane ya cika ne bayan sun sace wasu yara kanana uku daga garin Zuru sannan suka kai su jihar Anambra domin su siyar da su.
Gwamna Bagudu ya ce an kama Moses da Mrs Nwankwo ne lokacin da suke kokarin siyar da su yaran da a cikinsu har da wasu tagwaye.
Ya yabawa namijin kokarin da jami’an tsaron suka yi sannan ya bayyana cewa za a hukunta wadannan mutane kamar yadda yake a doka.
Bagudu ya yi kira ga iyaye da su rika sa ido a kan ‘ya’yan su.
Wasu daga cikin iyayen yaran da aka sace Yusuf Umar da Rabi’u Kabiru sun mika godiyar su ga gwamnan Bagudu, kungiyar ‘yan banga da jami’an tsaro saboda dawo musu da ‘ya’yan su da aka yi.
Yin garkuwa da yara na neman zama ruwan dare a Najeriya domin idan ba a manta ba a watan Oktoban da ya gabata ne aka sako dalibai ‘yan mata hudu da malaman su biyu da aka yi garkuwa da su daga makarantar sakandaren ‘Engraver’s College’ dake Kaduna.