TARIN DABBOBI: Muna rokon gwamnati ta yi wa shanun mu rigakafi – Kungiyar Miyetti Allah

0

Kungiyar Miyetti Allah ta kasa ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta yi wa shanun dake kasar nan rigakafin cutar tarin dake kama dabobbi wato ‘Bovine Pleuropneumonia (CBPP)’ a kasar nan.

Babban sakataren kungiyar Othman Ngelzarma ne ya yi wannan kira a Abuja ranar Laraba.

Ya ce yin allurar rigakafin cutar ne kadai hanyar dakile yaduwar cutar. Ya kara da cewa an samu rahotan bullowar cutar a jihar Bauchi da babban birnin tarayya, Abuja sannan zuwa yanzu an rasa shanu akalla 2000.

“ Muna kira ga gwamnati da ta gaggauta kawo mana dauki kafin cutar ya yadu zuwa wasu jihohin kasar nan.

Cutar tarin dake kama dabobbi da ake kira ‘Bovine Tuberculosis’ cuta ce dake hana dabba numfashi dakyau idan ya kamu da cutar.

Likitocin dabobbi sun bayyana cewa cutar ta fi kama shanu ne amma sauran dabobbi kamar su akuya, rago, tunkiya, kare, mage har da ma mutane za su iya kamuwa da cutar a dalilin zama kusa da dabbar da ta kamu da cutar.

Alamun kamuwa da cutar sun hada da tari, mura, zazzabi da sauran su.

Likitoci sun gargadi mutane da su rika dafa nama sosai tubus kafin a ci. Sannan idan an siyo dabba a tabbata likitan dabobbi ya duba daban kafin a hadashi da sauran dabobbi a gida.

Bayan haka kuma sun bada shawara da cewa a duk lokacin da dabba ya kamu da mura a rika killace shi kadai wato a raba shi da sauran dabbobin. Sannan arika yi wa dabbobi alluran rigakafi na cututtuka.

Idan ba a manta ba watan Yulin da ya gabata ne Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta karyata bullowar cutar tarin dabobbi wato ‘Bovine tuberculosis’ a Najeriya.

Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu ya yi kira ga mutane da su yi watsi da wannan mangana yana mai cewa babu gaskiya a abun.

Ya ce wasu ne ke yada irin wadannan labaran karya a kafafen sada zumunta na Whatsapp da facebook a yanar gizo cewa cutar ya bullo a Najeriya. Sannan har wai shugaban kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ya yi kira ga mutane da su nisanta kansu daga cin naman sa.

Ihekweazu yace domin karin bayani za a iya tuntubar su a shafinsu ta yanar gizo a www.ncdc.gov.ng, ko kuma a shafinsu na tiwita ko facebook.

Share.

game da Author