Zango ya dauki nauyin karatun wasu marayu da ‘ya’yan marasa galihu 101

0

Fitaccen jarumin wasan kwaikwayo na Kannywood kuna mawakin zamani Adam Zango ya cira tuta inda aka rika yi masa ruwan Allah yayi Albarka a dalilin biyawa wa wasu yaran talakawa da marayu kudin makaranta tun daga babban sakandare na daya zuwa na uku.

Hukumar makarantar ta rubuta wasikar godiya ga Zango a madadin makarantar da iyayen yaran da yayi wa goma ta arziki.

” Muna mika matukar godiyar mu ga Adam Zango kan wannan kokari da yayi na biya wa dalibai har 101 kudin makaranta tun daga ajin babban sakandare 1 zuwa na uku. Makarantar Farfesa Ango Abdullahi dake Zariya na mika godiyar ta a madadin ta da iyayen wadannan yara.

Adam Zango ya biya wa yara 101 har naira Miliyan 46,714,520.

Da yake amsa addu’o’in da aka rika yi masa, ya ce yayi haka ne domin ya taimakawa wadanda basu da karfi ko kuma halin iya kai yayan su karanta.

Ya ce zai ci gaba da yin haka domin tallafa wa marasa karfi a fadin Najeriya.

Share.

game da Author