‘Yan sumogal da barayin mai ku kuka da kan ku – Inji Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kakkausan gargadin cewa hukuma da jami’an tsaro za su kara sa ido wajen damke ‘yan sumogal da barayin mai.

Ya yi wannan bayani a cikin jawabin sa ba Ranar ‘Yanci a yau Talata, tare da nanata cewa, “Najeriya marhabin da duk wani tsarin cinikayya tsakanin kasashe. Amma na za ta ci gaba da yarda ana shigo ma ta da kayan sumogal a cikin kasa na.”

Buhari ya ce da masu satar danyen man fetur da masu satar tataccen fetur su na fita da shi waje su na sayarwa, duk su kuka da kan su.

Haka su ma masu shigo da kayan da aka hana shigowa da su, duk za a rika kama su ana gurfanarwa tare da hukunta su.

Cikin jawabin, a baya sai da Buhari ya kara jaddada aniyar gwamnatin sa wajen kare lkan iyakokin kasar nan da kuma cikin gida da Yankin Neja Delta.

Sannan kuma ya kara yin gargadin cewa gwamnati ba za ta sassauta wa masu sumogal din kayayyakin da aka haramta shigo da su daga waje ba.

Ya ce sumogal harkar karya tattalin arziki ce, wadda gwamnati ba za ta amince da ita ba.

Share.

game da Author