Safiya Ahmad ta lashe gasar Hikayata ta BBC Hausa

0

Marubuciya Safiyya Ahmed ne tayi zarra a gasar Gasar Rubutu ta Mata ta Hikayata ta BBC Hausa, 2019.

Safiya wadda ‘yar asalin karamar hukumar Zariya ce ta yi nasara da labarin ta mai suna ‘Maraici’.

Shidai Maraici labarin wata baiwar Allah ce da ta rasa mahaifinta tun tana karama. Hajiya Babba ta goya ta har takai minzalin aure daga nan ta yi mata aure. Wannan aure bai dore ba daga karshe dai mijinta ya sake ta. Ita kuma Hajiya Babba ta yi mata korara rashin mutunci bayan auren ya kare.

Wannan Labari shine ya fi burge alkalan wannan gasa.

Wadda ta zo na biyu kuma ita ce Jamila Rijiyan Lemo. Labarinta mai taken “Ba A Yi Komai Ba” ya ba da labarin yadda mata ke wahala ne a gidajen auren su saboda basu haifi ‘ya’ya maza ba.

Sannan labarin da ya zo na uku shine labarin Jamila Babayo mai taken “A Juri Zuwa Rafi”. Shi dai wannan labarin ya nuna yadda masu kudi ke cin zarafin yara kanana ne kuma babu wani abu da ake yi musu. A wannan labari mahaifiyar wannan yarinya, Laraba ta lashi takobin sai tabi wa ‘yarta hakkinta a wannan wuri.

Da take tattaunawa da PREMIUM TIMES, taurariya Safiya Ahmad ta bayyana cewa wannan rubutu da tayi, ba kawai ta yi shi bane don jin dadi sai don nuna wa mutane yadda Maraici kan canja rayuwar mutum zuwa wani yanayi na kuncin rayuwa da rashin jin dadi.

” Ni dinnan marainiya ce. Tun da mahaifina ya rasu na shiga wani irin yanayi na rayuwa da babu dadi. Irin labarin da na rubuta zai nuna wa mutane halin da marayu kan fada idan musamman iyayen su suka rasu suka barsu a hannun wasu.

Safiya ta yaba wa BBC Hausa bisa wannan dama da take ba mata domin nuna kwazonsu wajen karatu.

Jamila Rijiyan Lemo da Jamila Babayo da suka zo na biyu da na uku sun bayyana cewa lallai BBC ta cancanci yabo a dalilin samar wa mata wata kafa da za su rika nuna bajintarsu a harkar rubuce-rubuce.

” Wannan abu da BBC Hausa suka kirkiro ya cancanci ya bo matuka. Muna godiya da wannan dama da ake ba mata marubuta.

Wadanda suka yi alkalancin gasar dai su ne Dokta Aliya Adamu, malama a Jami’ar Jihar Sokoto, kuma kwararriya a kan Tarihin Adabi a Nazarin Harshen Hausa, da Hajiya Bilkisu Salisu Ahmad, fitacciyar marubuciyar nan da masu sha’awar rubuce-rubucenta suke kiran ta Aunty Bilki, da kuma Malama Bilkisu Yusuf Ali, marubuciya kuma mai nazari a kan adabin Hausa, kuma malama a Jami’ar Al-Qalam da ke Katsina, a Najeriya.

Wadannan alkalan sun zabo labaran uku ne daga cikin 25 din da aka tura masu.

Kafin nan sai da aka fitar da labarai 30 daga cikin sama da 300 da aka shigar a bana.

Kuma ko wanne labari daga cikin 30 sai da ya cika ka’idojin shiga gasar, wadanda suka hada da kasasncewa kagagge, da kasancewa marubuciyar ce ta rubuta shi, da kauce wa batanci da zagi, da amfani da ingantacciyar Hausa, da sauransu.

A cewar Malama Bilkisu Yusuf Ali, “Za ki ga wani a cikin ka’idojin ne yake faduwa—labarin da a ce ya bi wadannan ka’idojin dakidaki, da sai ki ga watakila shi ne zai yi nasara”.

Bayan nan kuma alkalan sun yi amfani da wadansu ma’aunai don tantance labaran.

Wadannan ma’aunai dai sun hada da salo, da hawa, da sauka, da rike mai karatu, da farkon labari, da sauransu.

Duk wadda ta yi nasara ita ce za ta zama ta hudu a jerin gwarazan gasar, wacce aka fara a shekarar 2016, kuma za ta karbi kyautar kudi dala 2,000 da lambar yabo.

Marubuciyar da ta zo ta biyu kuma za ta karbi kyautar kudi dala 1,000 da lambar yabo, sannan wadda ta yi ta uku za a ba ta kudi dala 500 da lambar yabo.

Share.

game da Author