‘Yar shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Zahra Buhari, ta bayyana wa taron bukin karrama wadanda suka yi nasara a gasar Hikayata ta BBC Hausa da aka yi a ranar Juma’a Abuja cewa dalilin da ya sa Hausan ta bai nuna ba shine yadda tun suna yara suka fara cudanya da turawa.
Gasar wanda BBC Hausa ta ke shirya wa duk shekara ya samu halarcin manyan baki ciki harda Zahra Buhari.
A jawabin da ta yi dakin taron na Ladi Kwali dake Otel din Sheraton, Zahra ta yabawa wadanda suka yi nasara baya ga jinjina wa BBC Hausa da ta yi bisa shirya irin wannan gasa musamman don ci gaban mata.
” A kullum muke magana da baban mu sai ya rika gyara mana Hausa. Tun Ina karama na bar gida, muna cudanya da turawa shine yasa bamu iya hausa haka ba. ”
Kalli nan: [youtube https://www.youtube.com/watch?v=GZz-P6N0bug&w=560&h=315]
Discussion about this post