Majalisar Tarayya ta ce sojoji su dakatar da Shirin Tantance Matafiya Kan Titi

0

Majalisar Tarayya ta nemi Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya da ta dakatar da Shirin Tantance Matafiya kan Titinan Najeriya da ta yi niyyar farawa a fadin kasar nan, a ranar 1 Ga Nuwamba.

Yayin da Majalisar ta amince da wani uzuri da Shugaban Marasa Rinjaye, Ndudi Elumelu ya gabatar, ta nemi kada sojoji su fara shirin a kasar nan baki daya.

Elumelu ya ce shisshigi ne kawai da kuma neman kara dora wa kai ‘Dutsin Dala ba gammo’, a ce sojojin kasar nan su kinkimo aikin tare hanyoyi a fadin kasar nan wai da sunan tambayar I.D cards din matafiya, saboda batun tsaro.

Ya ce idan sojoji suka yi haka, to sun tauye hakkin ‘yan Najeriya da Doka Sashe na 217 na Karamin Sashe na 2(c da d) ya ba su.

Shugaban Marasa Rinjayen, wanda dan PDP ne, ya kara da cewa batun I.D cards batu ne na Hukumar Bayar da Katin Shaidar Dan Kasa, NIMC da kuma sauran jami’an tsaro, ba wai sojoji ba.

Shi ma Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye, Toby Okechukwu, cewa ya yi wannan wani giringidishi ne da kuma kara wa kai wani nauyi, alhalin ga wasu kalubale a gaban sojojin. Ya ce ai da jami’an tsaron, amma ba su iya hana Boko Haram ba.

Shi ma Dan Majalisar Tarayya Honorabul Ahmed Jaha, cewa ya yi wata sabuwar wahala ce da kuma kuntata wa matafiya kawai sojoji ke neman haifarwa a kasar nan.

” Daga Abuja zuwa Maiduguri tafiyar awa 14 ce. To kwana nawa kenan ake so matafiyi ya shafe kafin ya kai, idan zai rika tsayawa kowane shingen sojoji domin ya bi layin tantance shi ta hanyar nuna I.D card din sa?” Inji Hon. Jaha.

Sojoji sun bayyana cewa sun yi nufin fara neman matafiya su nuna musu katin shaida ne domin kama batagari, ‘yan Boko Haram, ‘yan fashi da makami, barayin shanu, masu garkuwa da mutane da sauran masu laifuka.

Sun bayyana cewa tuni su ka fara wannan tsari a yankin Arewa maso Gabas, kuma ya na samun karbuwa, domin jama’a na bayar da hadin kai.

Sai dai dai kuma fara shirin gadan-gadan a fadin kasar nan, ya janyo korafe-korafe da kuma suka daga bakin ‘yan Najeriya, abin da har ya kai Majalisar Tarayya kiran sojoji su dakatar da fara shirin.

Share.

game da Author