Ministan Harkokin Ruwa, Sulaiman Adamu, ya bayyana cewa yankunan jihohin Tsakiyar Najeriya da ake kira ‘Middle Belt’ ne aka fi yin bahaya a fili a kasar nan.
Adamu bai ambaci sunayen jihohi ba, amma yankin ‘Middle Belt’ din da ya ke magana, ya kunshi jihohin Nasarawa, Neja, Kwara, Benuwai, Filato da kuma sassan garuruwan da ke karkashin Gundumar Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Ministan ya koka dangane da irin yadda ake yin bayan-gida barkatai a Najeriya. Adamu ya ce daga cikin Kananan Hukumomi 774 na kasar nan, cikin 14 ne kadai jama’a ba su yin kashi a waje.
Adamu ya bayyana wannan abin takaicin a jiya Litinin, lokacin da ya ke kare kasafin kudin ma’aikatar sa a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa.
Sai dai kuma Adamu bai bayyana sunayen kananan hukumomin 14 ba a gaban kwamitin da ya yi wa bayanin.
Ya ci gaba da cewa a Najeriya akwai gagarimar matsalar karancin wuraren bahaya da ban-dakuna a garuruwa da yankuna.
Sai ya yi kira ga gwamnatoci da ‘yan kasuwa su rika gina ban-dakuna a garuruwa da birane, inda ya ce akalla mutane milyan 47 a kasar nan me fama da matsalar rashin ban-dakuna.
Idan ba a manta ba, wata kungiya mai suna WASH NORM, a karkashin Hukumar UNICEF ta duniya, ta gudqnar da bincike cewa a duniya, kasar Indiya ne kadai aka fi Najeriya yawan masu tsuguno a waje su na kantara kashi.
An gudanar da wannan bincike kuwa tare da hadin guiwar Hukumar Kudiddigan Alkaluma ta Kasa, wato NBS, da ke Najeriya.
Sauran kasashen da ke bin Indiya da Najeriya, akwai Ethiopia, Indonesia, Pakistan, China, Nijar, Sudan, Chadi da kuma Mozambique.
Su ne kasashe 10 mafi munin kantara kashi a bainar jama’a a duniya.
Adamu ya ce gwamnati ta fara shelar wayar wa mutane kai dangane da illar wannan matsalar.