Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku ta Kasa, NCS, ta bada sanarwar cewa an samu nasarar kamo daurarru 25 daga cikin 122 din da suka tsere daga Gidan Kurkukun Koton Karfe.
Daurarrun dai sun tsere ne yayin da ambaliya ta mamaye gidan kurkukun, har ta fara shiga dakunan da daurarru Duke da kuma wasu ofisoshi.
Ambaliyar wadda ta mamaye har kan bangon gidan, ta yi sanadiyyar daurarru 123 ficewa da karfin tsiya daga kurkukun.
An bayyana cewa ambaliyar ba ta ci rai ko daya daga cikin daurarru 227 da ke kurkukun ba.
Kakakin Yada Labarai na Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku ta Kasa, Francis Enobore, ya ce ana kokarin gano sauran 97 da har zuwa lokacin rubuta wannan labari, jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda, jami’an gidan kurkuku, ‘Civil Defence’ da ‘yan sintiri ke ci gaba da neman su.
Enobore ya ce daga cikin daurarrun 227 da ke gidan, 122 ne suka tsere, amma an kamo 25, saura 97 ake nema. Akwai kuma wasu 105 da ba su yi kokarin guduwa zuwa ko’ina ba.
[04:19, 30/10/2019] Ashafa Numbers: Idan ba a manta ba, cikin watannin baya ne Shugaba Muhammadu Buhari ya bada sanarwar canja wa Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku ta Kasa suna, daga ‘Nigerian Prison Services’ zuwa Nigerian Correctional Services.
PREMIUM TIMES HAUSA ta ji daga wata kwakkwarar majiya cewa a yanzu haka ana vi gaba da bayar da horo ga sabbin ma’aikatan gidajen kurkuku da aka dauka.
Sannan kuma za a gyara tsarin daure masu laifi a gidajen kurkuku. Majiyar ta tabbatar da cewa za a gina kananan gidajen kurkuku a kananan hukumomi, yadda za a rika rage cinkoso tare da daina gwamutsa masu kananan laifuka wuri daya da rikakkun ‘yan fashi da makami.