Mahara sun yi garkuwa da jami’in NSCDC da yara biyu a Abuja

0

Dagacen kauyen Dafara dake karamar hukumar Kuje a babban birnin tarayyan Najeriya Abuja Makeri Joseph ya bayyana cewa wasu mahara sun kashe mutum daya sannan sun waske da ma’aikacin hukumar NSCDC da ‘ya’yan sa biyu.

Joseph ya bayyana wa manema labarai cewa wannan abin ban tsoron ya auku ne a makon jiya.

Wannan shine karo na biyu da ake garkuwa da mutane a karamar hukumar Kuje a cikin wannan mako.

Idan ba a manta ba a ranar Litini ne wasu ‘yan bindiga suka sace mutane tara bayan sun harbe wani Jami’in tsaro na NSCDC daya.

Bayan haka a wata takarda da rundunar ‘yan sandan Abuja ta raba wa manema labarai kakakin rundunar Anjuguri Manzahp yace rundunar ta hada hannu da sauran jami’an tsaro domin ganin an ceto wandannan mutane da aka sace.

Ya ce rundunar za ta dauki matakai domin ganin ta dakile miyagun aiyukka irin haka a Kuje da Robuchi.

Manzahp ya ce rundunar za ta hada hannu da masu ruwa da tsaki da dai sauran mutane domin kawo karshen miyagun aiyukka a Abuja.

Share.

game da Author