An cafke ‘Yan bindigan da suka kashe sojoji biyar a jihar Filato

0

Rundunar ‘Operation Save Haven (OPSH)’ dake aiki a jihohin Filato da Bauchi ta bayyana cafke maharan da suka kashe wasu sojoji biyar a jihar.

Kwamandan rundunar Austine Agundu ya sanar da haka ranar a garin Jos.

Agundu yace rundunar OPSH ta cafke wadannan mutane ne a maboyar su dake kauyen Bet a karamar hukumar Birikin Ladi.

Ya ce maharan sun tabbatar cewa su ne suka kashe sojoji biyar dake aiki da OPSH tsakanin ranakun 6 da 28 ga watan Satumba a kauyukan Nding-Sesut,kauyen Fan da Kwanan Fulani.

“Sannan binciken da muka gudanar ya nuna cewa akwai sauran abokan aikin wadannan mahara dake boye a wasu yankunan arewacin kasar nan.

Bayan haka Agundu ya ce rundunar ta samu nasaran kama mutane uku da suka shahara a yi wa mutane fashi a cikin mota ko keke NAPEP wato ‘OneChance’.

Ya ce rundunar ta kama Martins Obioha, Henry Okezie da Eloka Uzokwe a hanyar Rukuba a lokacin da suke kokarin yi wa wata mata mai suna Mary Ezekiel sata a cikin keke NAPEP.

Ya yi kira ga mutane da su ci gaba da hada hannu da rundunar domin ganin an samu nasaran kawar da miyagun aiyukka a jihar.

Share.

game da Author