BOKO HARAM: ‘Ba za mu daina kashe mutane ba’ – Inji Shekau

0

Shugaban kungiyar Boko Haram mai kai hare-haren ta’addanci, Abubakar Shekau, ya fito bayan likimon da ya yi na tsawon lokaci, inda ya maida wa Gwamnan Jihar Barno, Babagana Zulum martani kakkausa.

Shekau ya maida wa Gwamna Zulum martani ne, bayan da gwamnan ya fito ya yi bayanin cewa ‘yan Boko Haram su ajiye makaman su, su yi saranda domin su samu shiga cikin Shirin Afuwar Gwamnatin Tarayya.

Cikin wani sakon minti 18 da aka rika yada muryar Shekau na magana a cikin harshen Kanuri da kuma Hausa, shugaban na Boko Haram ya karyata Zulum wanda ya ce wasu mabiya Boko Haram din da aka tilasta wa shiga ba da son ran su ba, sun gaji da yakin da ake yi wanda ya ki ci ya ki cinyewa.

Shekau ya ce babu wani mamba din kungiyar su ko daya da ya gaji da yaki, kuma za su ci gaba da yakin har lokacin da mutuwa za ta dauki ran su.

Wannan ne bidiyon farko da Shekau ya fitar tun bayan watanni masu yawa da aka daina jin labarin sa.

Can a tsakiyar bidiyon kuma sai Shekau ya saka muryar Gwamna Zulum inda ya ke jawabi a gaban jama’a ya na kiran ‘yan Boko Haram su yi saranda, domin su ci amfanin shirin afuwa na gwamnatin tarayya.

Ba a dai san yadda Shekau ya samu wannan bidiyo ba, amma kuma dama ana yada ji-ta-ji-ta cewa wasu mambobin Boko Haram na yin basaja, a cikin sansanin masu gudun hijira.

Gwamna Zulum kuma an ce akwai su a cikin wasu sansanin gudun hijira da Zulum ya kai ziyara kwanan nan.

A jawabin na sa, Zulum ya karkare da jawo wata aya daga Alkur’ani, inda ya nuna cewa, “Allah mai gafara ne”, don haka Boko Haram su tuba.

Sai dai kuma Shekau ya fito ya kalubalanci gwamnan.

Fassarar Kalaman Shekau

“Na yi tunanin fitowa na aika wannan sakon domin yin matashiya daga kalaman da kalaman da Gwamnan Barno ya yi, inda ya ce wai wasu mayakan mu da mu ka tilasta su na yaki, sun gaji da yakin.

“Sannan kuma saboda haka wai gwamnati ta fito da shirin “operation safe corridor, inda mambobin mu da suka tuba za su samu tallafi.

“Ina so na sanar wa gwamna cewa ba mu kai ga gajiya ba tukunna. Mu yanzu ma mu ka fa. Mu fatan mu shi ne mu mutu a wurin yaki. Mu na kan hanyar samun nasara. Da girman Allah a kan wannan tafarki za mu mutu. Mu nan dai har yanzu ana fafatawa da mu.

“Ina so ka sani a cikin musulunci, ba za ta kaba samun gafarar Allah ba , idan ka mutu b aka ka cikin addinin musulunci.

“Gwamna ya sani cewa musulunci ba addinin jihar Barno ba ne. Ba na jihar Yobe ko Jamhuriyar Nijar da Kamaru ba ne. Addinin Allah ne. Shi ya sauko da shi ga Annabi (SAW).

“A kan wannan dalili, jama’a su daina fassara ayoyin Alkur’ani a birkice. Misali, ayar da gwamna ya jawo game da karbar tuba, ba daidai ya jawo ta ba, kuma bai dora ayar daidai da inda ya dace a dora ta ba. Haba gwamna. Wannan ai bain kunya ne a gare ka.

“Ba mu ne za mu tuba ba; gwamnan ku gwamnan Barno shi ne ya kamata ya tuba. Ba za ta taba shiga aljanna da abin da ka ke aikatawa a yanzu ba.

“Ita duniya cike ta ke da masu neman abin duniya ba ta hanyar addinin Allah ba. Amma ita aljanna ta wadanda suka yi aikin shiga aljanna ce, wadanda su ka bi shiriyar Allah. Mukami ko dukiya ba su iya sai wa kowa shiga aljanna. Al’ummar Jihar Barno ku tubaku koma kan turbar Allah.

“Ita kuwa dimokradiya kafirci da shirka ce. Democracy ma’anar ta “shaidanu da dujajalai.” Doka ce wadda mutum ya yi. Shi kuwa Allah ya haramta mana bin dokokin da mutum ya yi. Allah ya umarce mu mu kada mu bauta wa kowa sai shi kadai.

“Amma ku ku na bin dokar kwansitushin, alhali ga Alkur’ani. Har gara a turbude mutum a karkashin kasa da ya rayu a cikin wannan gurbataccen karni.

“Wannan shi ne sako na ga al’ummar jihar Barno, dangane da jawabin da gwamnan su ya yi.

“Ina kara jaddada cewa duk dan kungiyar mu da wai ya fita saboda ya gaji, to ya na bata lokacin sa ne kawai. Su sani cewa ko mu ai da Allah mu ka dogara a dukkan al’amurran mu. Duk wanda ya san Alkur’ani ba zai yarda ya yi ko da rayuwar sakan daya a cikin wadancan kafirai ba.”

Share.

game da Author