KWACE GIDAJE: EFCC ta yaudari mai shari’a -Saraki

0

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa Hukumar EFCC ta nunke mai shari’a baibai, har ya amince ya bada umarnin rike masa gidanje biyu, rikon wucin-gadi da ke Ikoyi, Lagos.

A ranar Litinin PREMIUM TIMES ta kawo rahoton cewa Babbar Kotun Tarayya, Reshen Lagos, ta bayar da umarnin a kwace gidajen Saraki zuwa lokacin da za a ga yadda hukuncin shari’a zai kasance.

An bayar da wannan umarnin ne a kotun, bayan da EFCC ta shigar da rokon a kwace gidajen, kwacewar wucin-gadi. Gidajen guda biyu dai su na unguwar Ikoyi ne Lagos.

Mai Shari’a Mohammed Liman, wanda ya bada umarnin kwace gidajen, ya kuma bayar da wa’adin kwanki 14 ga duk wani mai ruwa da tsaki ko shi maigidan ya bayar da bayani ga kotun na dalilin da zai sa ba za a rike gidajen na sa biyu ba.

Wato ya gabatar da dalilin da zai sa kotu ta fasa bayar da umarnin rike gidajen.

EFCC ta yi zargin cewa Saraki ya yi amfani da kudin da ta yi zargin ya kamfata daga aljihun gwamnatin Jihar Kwara, a lokacin da ya ke gwamna, ya sayi gidajen.

Sai dai kuma a na sa martanin ga hukuncin kotun, Saraki ya yi magana ta hannun kakakin yada labaran sa, Yusuf Olaniyonu cewa: “Saraki ko lauyoyin sa babu wanda ya san cewa EFCC ta rubuta rokon kotu ta ba ta umarnin rike gidajen na sa biyu.”

Hakan kuwa inji Saraki ya kauce wa ka’idar shari’a a kotu.

Saraki ya kara da cewa “Kotun Tarayya ta Lagos ba ta san da cewa Kotun Koli cikin watan Yuli, 2018, ta yanke hukuncin cewa kudin da Saraki ya sayi gidajen biyu da su, ba kudin sata ko harkalla ba ne, kamar yadda EFCC ta yi ikirari.”

Ya kara da cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, tuni ta bayar da umarnin cewa “ta dakatar da EFCC daga katsalandan a kokarin karbar wadannan gidaje biyu na Saraki.

EFCC ta fara binciken Saraki, inda ta fara neman sani daga Gwamnatin Jihar Kwara na takamaimen kudin da ake biyan Saraki na komai da komai a lokacin da ya ke gwamnan jihar.

Idan ba a manta ba, an kai Saraki kara a Kotun CCB dangane da gidajen cikin 2017.

“Mun tabbatar da cewa EFCC yaudarar Babbar Kotun Tarayya ta yi har ta yi gigiwar bayar da umarnin wai a kwace gidajen biyu tukunna.

“Wadannan gidaje masu lamba 17A da 17B, a kan su ne aka fara kai Saraki kara a CCB, amma da shari’ar ta kai Kotun Koli, a ranar 6 Ga Yuli, 2018, Kotun Koli ta bai wa Saraki gaskiya.

“Don haka mu dai mun san duk wani kicifin da aka yaudari wata kotu ta yanke danyen hukunci a kan wanda Kotun Koli ta rigaya ta yanke, to ba abu ne mai dorewa ba.

“Wannan dalili kawai ya ishe mu gabatar wa kotu cewa ta soke wannan umarnin da ta bai wa EFCC kwace gidajen. Don haka mu na kira ga ‘yan uwa, abokan arziki da sauran masoyan Saraki su kwantar da hankalin su. Wannan hukunci da Kotun Tarayya ta yanke, digirgire ne.”

Share.

game da Author