PREMIUM TIMES ta tura wakilin ta ya yi shigar-burtu, aka maka shi kotu, aka tura shi kurkuku, amma ba a san ya shiga ne domin tabbatar da zarge-zargen da ake yi na munanan aikata ayyuka a cikin kurkukun ba. Ga abin da FISAYO SOYOMBO ya gano.
‘MAI KUDI SARKI NE A KURKUKUN IKOYI’
A kurkukun tun farkon kai ni na ji wasu jami’ai su na tattauna irin badalaka da harkallar da ake aikatawa, sai na ga tunda ba su yi waicin gani na ba, ko jin nauyin ina kusa da su, amma su na wannan kasassaba ba, sai ni ma na matsa na tambaye su abin da zan dan bayar na cin hanci domin a ba ni wurin kwanciya mai dan dama-dama.
“Idan ka na da naira 30,000 za a iya ba ka daki, akwai kuma na naira 100,000, kai har na 150,000 ko naira milyan 1.5 duk akwai.
“Domin ko lokacin da aka kulle Ayodele Fayose a nan kurkukun Ikoyi, shin ka na zaton a cikin wane irin kurkuku aka tsare shi?
“Aboki na, kada ka damu. Idan ka na da kudi to fa ba za ka taba shan wahala a cikin kurkukun nan ba.”
YADDA MA’AIKATAN KOTU DA JAMI’AN KURKUKU KE SHIRYA BELI NA HARKALLA
Tun ba a wuce awa biyu rak da bayar da beli na ba, sai wani jami’in Gidan kurkuku ya tunkare ni ya ce, “shin ka fara shirye-shiryen beli dai ko?” Na ce masa lauya na ya na kan kokarin beli na.
“To ai ni ina da wani lauya wanda zai shirya maka yadda zai yi belin ka a yau din nan idan ka na bukata. Kai a yanzu ma haka idan ka amince, kafin a karasa da kai kurkuku an gama komai. Ba ma za mu kai ka kurkukun ba.
Kafin ka ce me, har lauyan wani mai kimanin shekaru 40 haka ya kawo kan sa.
Sai ya fara tambaya ta, mene ne laifin da na yi? Ya ce matsalar da ta dabaibaye laifi na duk za a iya shafe ta a yau din nan, amma fa zan kashe kudi.
Sai ya sake tambaya ta, “nawa Mai Shari’a ya ce ka biya a asusun ajiyar Rajistara?”
Na ce masa naira 300,000. Wato kowane mai beli mutum daya naira 150,000 kenan.
Na ce masa kudin sun yi yawa, ya zan dora har naira 50,000 a kowace naira 150,000? A karshe dai mu ka daddale a kan naira 170,000 kowane mai beli daya. Ya ce yanzu karfe 3:00 na rana, na hanzarta kiran a kawo min kudi na ba shi.
A karshe dai na ce ya ba ni lambar sa, sai gobe na sa a kawo kudin. Ban sake kiran sa ba, saboda ni dama muradi na shi ne a kulle shi a kurkukun Ikoyi.
Daga kuma ina tare da wata ‘yar na’ura, wadda na ke rikodin din duk wata magana da na yi da wani, da abin da ya rika faruwa tun daga kotu har cikin jami’an kurkuku.
An tura ni wani bangare na rikakkun masu laifi, domin su koya min hankali, lokacin da aka gano ‘yar na’urar da na ke daukar maganganu.
Washegari da safe, wani babban jami’in gidan kurkuku mai suna Sunkanmi Ijadunola, ya kira ni, ya nemi na fada masa gaskiyar ni kowane.
Amma ban fada masa gaskiya cewa ni dan jarida ba ne. Kafin sannan kuwa duk hankalin su ya tashi, saboda duk sun kalli bidiyon da na yi rikodin, wanda aka nuno yadda ake shirya harkalla da cuwa-cuwa a kotu da kuma irin wadda jami’an gidan kurkuke ke yi.
Da jami’in nan ya ga cewa ban fada masa gaskiya ba, sai ya ce to ya gane na yi rikodin ne don na gano yadda zan shirya tserewa. Ya ce na yi nufin aikawa da bidiyon ga abokai na ‘yan Boko Haram domin su zo su ceto ni. Ya ce wai ni dan Boko Haram ne.
Daga nan sai ya sa aka samo masa wata zabgegiyar tsabga, ya sa na tube riga ta da wando. Daga ni sai singileti da dan kamfai. Ya yi ta zabga min bulala, har ya yi min jina-jina. Duk da haka dai ban yarda na ce musu ni dan jarida ba ne.
Kwana dayan da na kara yi, na kara bude ido na dangane da irin tabargatsa, bahallatsa da harkallar da ake aikatawa a cikin kurkukun.
Duk wanda za a kawo kurkuku, zai bayar da naira 1,000 cuwa-cuwa ga wani jami’ain kurkuku a lokacin da zai bayar da ajiyar kudin sa. Haka na bayar da naira 1,000 daga cikin naira 7,200 da aka kai ni kurkuku tare da ita.
ASIRI NA YA TONU
Bayan sun gano akwai wasu abokan aiki na biyu da su ma aka kulle a kurkukun, na ga dai ba yadda zan yi sai nawai na ce musu ni dan jarida ne, don kada su ma su sha irin bakar azabar da na sha.
Abincin da ake bai wa daurarru a kurkuku, ko wanda aka yanke wa hukuncin kisa, kuma ake shirin kashe shi yanzu-yanzu, bai kamata a ce an ba shi abincin ba.
DA NAIRA N10,000 SAI A SHAFE TARIHIN ZAMAN KA A KURKUKU
“Na yi wani dan kusanci na takaitaccen lokaci da wani dan ‘yahoo boys’, wanda ya ce min idan ka bada cin hancin naira 5,000, za a iya bari a shigo maka da duk wani abin da ka ke bukata.
“Idan ka na bukata, za ka biya naira 10,000 a hada ka da wanda zai maka hanyar a shafe sunan ka daga kurkuku, tamkar ba a taba daure ka ba. Ko an nemi sunan ka ba za a taba gani ba.”
LUWADI, SHAN GIYA, KWAYA DA KWANA DA KARUWA A CIKIN KURKUKU
Idan wanda ke zaman gidan kurkuku a Ikoyi na da kudi, to akwai kwayoyi, gida da zai sha. Kuma ana neman maza sosai.
Sunayen dakuna ko kurkukun musamman na alfarma da ake ajiye masu kudi idan sun biya, akwai ‘Nicon Luxury’, wanda za ka biya naira 20,000 ko naira 50,000 a kowace rana.
“Idan ka na bukatar giya, taba, wiwi, kwaya ko ‘yan mata, duk za a kawo maka.
“Akwai AC a ciki, da kushin masu kyau da katifa. Amma fa a dakunan ya-ku-bayi za ku kai ku 118. Kuma an yi dakin ne domin ya dauki mutum 30 kacal. Wadanda ke cikin ‘Nicon Luxury’ kuwa sai masu kudi.
A na kai wa mutum karuwai har cikin kurkuku. Za ka biya kudi, a kira karuwa, ka kwanta da ita ka biya ta, ta kama gaban ta.
“Akwai muggan kwayoyi birjik a kurkuku, wadanda idan ba da hadin kan jami’an kurkuku ba, babu yadda za a yi a rika sayar da su a cikin kurkuku.
Muggan kwayoyin da za ka iya samu a cikin kurkuku sun hada da ‘Colorado’, Tramadol, refnol da sauran su. Amma an fi amfani da Colorado, wadda naira 5,000 ake sayar da ita a cikin kurkukun.
“Samun man shafa na Vasiline na da wahala a kurkuku. Amma ba shi da wahalar samu ga daurarrun da ke luwadi a cikin kurkukun na Ikoyi.
Jami’an kurkuku sun sani sarai daurarru na yin luwadi da junan su. Kuma su ne ke sayo musu Vasiline, domin duk wanda zai zo ziyara, sai an caje shi, ba a bari ya shiga da ko tsinken allura.”
A kurkukun Ikoyi dai babu wata maganar gyaran halin mai laifi ya zama nagari. Maimakon haka, kara kangarewa masu kananan laifuka su ke yi.
Wanda ya ce wanda aka dauke a can kan iya gyara halayen sa, to karya ya keyi. Kurkuku ba gidan gyaran mai gurbatacciyar tarbiyya ba ne. Sai ma kara dulmiya shi yin nitso cikin kogin aikata manyan laifuka idan ya fito kawai.
Discussion about this post