Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, ya bayyana cewa ba daidai ba ne da aka rika yayata cewa majalisa ta hana ‘yan jarida shiga zaman sauraren kare kasafin kudi da ake ci gaba da gudanarwa a Majalisar Dattawa.
Cikin wata sanarwa da kakakin Lawan, mai suna Ola Awoniyi ya sa wa hannu, wanda kamar martani ne ya ke mayarwa ga wasu rahotanni da wasu kafafen yada labarai na kasar nan su ka buga, Awoniyi, ya ce ba haka abin ya ke ba. Ba a hana manema labarai shiga ba.
Wasu kafafen yada labarai dai sun ruwaito cewa an hana manema labarai shiga sauraren kare kasafin kudin, wanda ake kiran shugabannin bangarori domin kowa ya kare kasafin kudin sa.
“Ba mu hana manema labarai shiga sauraren dukkan abin da mu ke yi ba.
“Ai mu na ma bukatar manema labarai domin su rika sanar wa ‘yan Najeriya abin da mu ke yi a majalisa. Ku ‘yan jarida ai abokan mu ne. Da aka ce mun hana ku shiga, ba daidai ba ne.”
Sai kuma Lawan din ya ce amma abin lura a nan shi ne, akwai wasu batutuwan da ke bukatar sirri, musamman idan sun shafi abin da ke bukatar sirrantawa a kasar nan, saboda wasu dalilai, kamar na tsaro, to shi ne sai a nemi uziri daga manema labarai.
“Ina tabbatar wa dukkan ‘yan Najeriya cewa dukkan abin da za mu yi a Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya, za mu wanda zai kawo wa kasar nan cigaba ne.
“Ni ba zan bayar da kai bori ya hau don a yi wani abin da zai cutar da kasar nan, ko ‘yan kasar nan ba.” Cewar Lawan.