Wata cuta mai lalata amfanin gona, da ta fantsama bagatatan a jihar Kebbi, ta haifar da asarar albasa ta kimanin naira bilyan daya.
Cutar wacce kala biyu ce, akwai zazzalu da kuma raba, kamar yadda shugabannin Kungiyar Manoman Albasa na jihar su ka bayyana.
Shugaban Kungiyar mai suna Bello Uba, ya shaida cewa cutar zazzalu ta na lalata albasar da ake cikin gonaki, kuma ta na bi har cikin rumbunan ajiya ta na lalata albasar da aka adana.
Ya kara da cewa cutar zazzalu da raba sun lalata albasar da ke cikin akalla gonaki 20,000.
Uba ya ce shekara da shekaru su na noman albasa, amma ba su taba ganin irin wannan ibtila’in cutar da ke lalata har albasa ba.
Dangane da magani kuwa, ya ce sutar ba ta da magani, domin sun yi iyakar kokarin su yin amfani da magunguna, amma ba a shawo kan cutar ba.
Sai dai kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Gona na jihar Kebbi, Muhammad Lawal, ya ce wannan labari bai je musu cewa wasu manoma sun dibga asara ba. Kuma ba su da labarin bullar cutar mai lalata albasa, amma dai yanzu za su gudanar da bincike.
A Arewacin kasar nan dai Jihar Kebbi ce a sahun gaba wajen yin riko da igiyar noman rani gadan-gadan, tun bayan kokarin da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fara yi a cikin 2016 wajen inganta harkokin noma.
Musamman noman shinkafa ya samu karbuwa a jihar, tun kusan shekaru uku da suka gabata.
Manoman jihar da dama sun ci moriyar karbar lamunin ga gwamnati ta rika bayarwa wajen habbaka aikin noma.
Sai dai kuma wasu manoman da dama sun yi korafin cewa yawanci ‘yan siyasa ne suka karbe lamunin, ba manoma na ainihi ba.