BOKO HARAM: Gwamnati ta janye korar da ta yi wa kungiyoyin ‘Mercy Corps’ da ‘Action Against Hunger’

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta janye korar da ta yi wa kungiyoyin bayar da agaji guda biyu daga Arewa maso Gabas.

Ministar Ayyukan Agaji da Inganta Rayuwar Jama’a, Sadiya Umar ce ta bayyana haka, a ganawar da ta yi da manema labarai, ranar Laraba.

Sadiya ta ce amma janyewar ta wucin-gadi ce, ba ta dindindin ba.

Ta ce, “Gwamnatin Tarayya ta janye korar da aka yi wa Kungiyar Bayar da Agaji da Taimakon Jinkai ta ‘Mercy Corps’ da kuma Kungiyar Hobbasar Yaki da Yunwa ta ‘Action Against Hunger.’

Cikin watanni biyu da suka gabata ne Hukumar Tsaron Sojoji suka kori kungiyoyin biyu, bayan sun zarge su da nuna goyon baya ga Boko Haram.

Sai dai kuma babu wasu hujjoji da sojojin suka bayar.

Kwanan nan kuma Karamin Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Mark Lowcork ya zo Najeriya, inda ya gana da manyan jami’an gwamnati.

A bayan ganawar ta su ce, Lowcork ya bayyana wa manema labarai cewa sun gana ne dangane da batutuwan da suka shafi ayyukan kungiyoyin agaji masu ayyukan jinkai a Arewa maso Gabas, kuma gwamnatin Najeriya ta janye dakatarwar da ta yi wa Mercy Corps da Action Against Hunger.

Share.

game da Author