‘Yan sanda sun damka ‘yaran da aka sato daga Gombe ga iyayen su

0

Rundunar ‘yan sandan Jihar Anambra ta bayyana cewa ta damka kananan yara biyu ga mahaifan su.

Yaran biyu, Wahab Yusuf mai shekaru uku da Mustapha Abdullahi mai shekaru biyu, wasu masu safarar kananan yara ne suka sace su ne daga Jihar Gombe, aka sayar da su a jihar Anambra.

‘Yan sanda sun bankado masu safarar wadanda mata ne su uku. An kama Blessing da yaran biyu.

Wannan ne karo na biyu da aka bakado masu hada-hadar sayar da yara. Cikin farkon Oktoba an bankado yadda aka saci wasu yara bakwai daga Kano, aka sayar da su a Anambra, su 9.

Tuni dai aka hada yaran da iyayen su, wadanda bayan an sayar da su, sai kuma aka maida su Kiristoci.

Wannan abu ya harzuka jama’a, har ta kai Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a yi bincike.

Shi ma Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya bada umarnin a yi binciken gano zargin da ake ci gaba da yi cewa akwai kananan yara har 47 da suka bace daga Kano, amma shiru babu labarin su.

An yi zargin an sayar da yaran a Jihar Anambra.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ma ‘yan sanda a jihar Kano sun kama wasu mutane ‘yan asalin jihar Imo dake satar yara kanana a jihar Kano suna saida su a can yankin inyamirai.

Wadannan mutane da aka kama da suka hada da mata, sukan sace yarane sannan su canja musu addini kafin su saida su.

Share.

game da Author