Wata gobara da har yanzu ba a tantance musabbabin ta ba, ta tashi a Ofishin Tattara Kudaden Harajin Cikin Gida na Gwamnatin Tarayya da ke Abuja.
Wutar wadda ta tashi yau Litinin da safe, ta cinye wani ofishi da ke kusa da dakin sayar da abinci, wanda ma’aikatar Hukumar ta FIRS ke sayen abinci.
Ofishin wanda ya kone, kamar yadda Kakakin Yada Labarai na FIRS ya bayyana wa PREMIUM TIMES, cewa, “gobarar karama ce kuma wani dakin ajiya ne guda daya kawai ta ci.” Haka Wahab Gbadamosi ya bayyana.
Dubban jama’a sun ga jami’an kashe gobara a kololuwar gini su na aikin fesa ruwan kashe gobara, yayin da hayakin da ke tashi ya tirnike hedikwatar Hukumar Tattara Kudaden Haraji.
Babban Jami’in Kashe Gobara Julius Opetunsin bai amsa kiran wayar wakilin ba, domin a ji irin ta’adin da gobarar ta haddasa.
Shi ma Gbadamosi ya ce a yanzu dai ba za a iya jin shin wasu muhimman takardu sun lalace ba ko a’a, sai nan gaba kadan.
Tuni dai Hukumar ta FIRS ta ce za ta binciki musabbabi.
FIRS dai nan ne Ofishin da ke karbar Kudaden haraji, kuma daga ofishin ne ake bijiro da harajin jiki-magayi da sauran hajari daban-daban.