A ranar Laraba, 30 Ga Oktoba ne Kotun Kotun Koli za ta fara saureren karar da dan takarar zaben Shugaban Kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya daukaka.
Atiku da PDP sun ki amincewa da kayen da suka sha a gaban alkalan Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa, wanda aka zaryas a ranar 11 Ga Satumba, 2019.
Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa ta bayyana cewa Atiku da PDP sun kasa gabatar da kwakkwatan hujjojin da su gamsar da kotun cewa INEC da APC sun tafka magudi a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 Ga Fabrairu, 2019.
Lauyan PDP Mike Ozekhome ne ya shaida wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho cewa a ranar 30 Ga Oktoba ce Kotun Koli za ta fara sauraren karar.
Atiku da PDP sun ce Kotun Daukaka Kararrakin Zabe ta kwafsa sosai wajen yanke hukuncin da suka ce ta yanzu wasu a karkace, wasu a gicce, wasu kuma a assake. Don haka ba a yi musu adalci ba, kuma ba su gamsu ko amince da hukuncin, wanda suka kira danyen hukunci ba.
Wannan ne matsakin karshe na yanke hukuncin wannan shari’a. Idan Buhari ya sake yin nasara a kotu, to sai dai Atiku da PDP su hakura.
Idan kuma Atiku ne ya yi nasara, to Buhari zai gaggauta kwashe kayan sa daga fada, Atiku da PDP su hau mulki.
Sai dai kuma a tarihin shari’ar zabe a Najeriya, jam’iyyar adawa ba ta taba yin galaba a kan shugaban da aka rigaya aka rantsar ba.
Shi kan sa Buhari a lokacin da ya ke adawa, sau uku ya na kai kara a kotu, har ya na danganawa da Kotun Koli cikin 2003, 2007 da 2011, amma duk bai yi nasara ba.