Sakamakon binciken da kungiyar ‘Malaria Futures For Africa (MalaFA) ta gudanar ya nuna cewa zai yi wuya kasashen Afrika su iya rabuwa da zazzabin cizon sauro nan da 2030.
Binciken ya kuma nuna cewa gaggauta ware isassun kudade domin yaki da cutar na daga cikin hanyoyin da zai taimaka wajen cin ma wannan buri a Afrika.
MalaFA ta gudanar da wannan binciken ne a kasashen Kudu da Saharan Afrika 15 wanda Najeriya,Ghana,Niger, Kenya da Ethiopia ke cikin wadannan kasashe.
Kungiyar ta ce babbar dalili gudanar da wannan binciken shine domin a gano matsalolin dake kawo koma baya a yaki da kawar da zazzabin cizon sauro duk da dimbin tallafin da kasashen Afrika ke samu.
A yanzu haka bayanai sun nuna cewa a duk shekara kasashen Afrika na yin asarar akalla dala miliyan 12 a dalilin zazzabin cizon sauro.
Matsalolin da binciken ya bankado
1. Tsara hanyoyin kawar da cutar da kungiyoyin bada tallafi daga kasashen waje ke yi wa kasashen Afrika.
Binciken ya gano cewa kungiyoyin bada tallafi na kasashen waje na bada kudade domin yaki da zazzabin cizon sauro amma da sharadin cewa sune za su tsara hanyoyin da ya kamata a bi wajen kawar da cutar wa kasashen Afrika.
Ma’aikatan fannin kiwon lafiya da aka tattauna da su sun bayyana cewa yin haka baya yiwuwa ganin cewa yadda wadannan kungiyoyin suka fahimci matsalar ba haka bane ke faruwa a kasashen Afrika.
Sun ce a dalilin haka ya sa duk wani doka da za a kafa basu iya yin tasiri.
2. Rashin yin amfani da tallafin da kungiyoyin kasashen waje suka bada yadda ya kamata.
Binciken ya gano cewa wasu kasashen Afrika na amfani da tallafin da kungiyoyin kasashen waje ke badawa a wasu matsalolin da kasashen su ke fama da su a maimakon yaki da zazzabin cizon sauro wajen gina tituna,samar da wutar lantarki da sauran su wandan hakan bai kamata ba.
3. Sama da fadi da kudade tallafin da kungiyoyin ke badawa.
Kungiyoyin bada tallafi daga kasashen waje sun koka da yadda mafi yawan kasashen Afrika ke wawush tallafin da suka samar musu.
4. Rashin shugabanin masu kishin kasa.
Rashin samun shugabanin masu kishin kasa a kasashen Afrika na daga cikin matsalolin dake sa gwamnatocin kasashen yin watsi da ire-iren wadannan ayyuka.
5. Rashin nuna aiyukkan da gwamnati da ma’aikatar kiwon lafiya ke yi na inganta kiwon lafiya
Daga nan jami’in kungiyar ‘Roll Back Malaria (RBM) Richard Kamwi ya bayyana cewa Nahiyar Afrika za ta iya cin ma burin ta na kawar da zazzabin cizon sauro nan da 2030 duk da cewa kasashen suns samun koma baya a yaki da cutar.
Kamawi ya ce ware isassun kudade domin yaki da cutar,hada hannu da hukumomi da bangarorin dake ciki da wajen kasashen su, gudanar da binciken da zai samar da ingantaccen hanyar kawar da cutar a kasashen su.