A wani mummunan harin kwanton-bauna da Boko Haram suka kai, sun kashe sojojin Najeriya 11 kuma suka jikkata wasu 14.
Wannan hari ya faru ne a lokacin da wasu zaratan sojoji 34 daga Bataliyar Aikin Musamman ta 154 dake kan aikin sintiri a Mauli zuwa Borgozo.
Majiya daga sojoji ta ce gumurzun yaki ya tirnike, tun wajen 11:25 na rana. Amma ba a san lokacin da yakin ya kare ba, bayan Boko Haram din sun gudu.
Yakin wanda aka yi a ranar 3 Ga Oktoba, an kuma rasa inda wasu sojoji biyu suke.
An kuma ce Boko Haram sun kwashi bindigogi samfurin AK47 11, na sojojin da suka kashe. Sun kuma gudu da motar da ake girka wa babbar bindigar kakkabo jiragen yaki.
Majiya ta ce an fara garzayawa da sojojin da suka ji ciwo a Sansanin Musamman na Benishiekh, daga nan kuma aka wuce da su Asibitin Sojoji na Maiduguri.
Mazauna kauyen sun tabbatar da ganin gawarwakin farar hula 15. Amma ba su tabbatar ta Boko Haram ba ce, ko kuma ta wadanda tsautsayi ya ritsa da su ba.
KARFIN BOKO HARAM BAI RAGU BA, inji Olumide Adesanya
Ganin yadda Boko ke yawan kai wa sojojin Najeriya hari ba kakkautawa, manazarci kan harkokin tsaro Olumide Adesanya, ya ce ko kadan karfin Boko Haram bai ragu ba, sai ma karuwa da ya yi.
“Yanzu sun ma kara karfi, sun daina jefa bama-bamai, sun maida hankali gadan-gadan su na kai wa sojojin mu hari a barikoki, sansanoni da kwanton-bauna a kan titi.
“Ni dai a gani na sun ma fi karfi a yanzu.” Inji Olamide Adesanya.
Idan ba a manta ba, makonni biyu da suka gabata.
Hukumar Tsaron Sojojin Najeriya na neman wasu sojoji 22 da suka arce daga filin gumurzun yaki da Boko Haram.
Sanarwar kamar yadda wata majiyar manyan jami’an soja ta sanar da PREMIUM TIMES, ta ce idan aka kama su za su fuskanci kwakkwaran hukunci, saboda gudu da suka yi ana cikin fafata yaki da Boko Haram.
Sun arce ne a lokacin da gungun Boko Haram suka kai hari a wani sansanin soja da ke kusa da garin Gubio, a ranar 29 Ga Satumba. Wani yankin na Gubio har yanzu a hannun Boko Haram ya ke.
Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES an kashe sojoji 18 a wannan hari da aka kai ranar Lahadi da ta gabata, 29 Ga Satumba. Sai dai kuma wannan jarida ba ta tabbatar da adadin wadanda aka kashe din ba.
Amma kuma manyan jami’an soja da suka gaggauta tantance barnar da aka yi, a karshe sun gano cewa babu sojoji 22 sun gudu. Kuma a karkaahin wani Manjo su ke.
An kai wannan hari ne wajen karfe 4:30 na yamma a ranar 29 Ga Satumba. Kuma tun a ranar aka nemi sojojin 22 aka rasa.
Yayin da babu gawar su, kuma aka hakikance ba kama su Boko Haram suka yi ba, an tabbatar da cewa tserewa suka yi.
Tun cikin watan Juli, 2018 Shugaban Sojojin Najeriya, Tukur Buratai ke nanata cewa duk sojan da ya gudu daga fagen fama zai fuskanci tsatstsauran hukunci.
Gudun da wasu sojoji ke yi daga filin daga na daya daga cikin manyan kalubalen da yaki da Boko Haram ke fuskanta a kasar nan.
Cikin Satumba, 2014, wajen sojoji 400 sun tsere cikin kasar Kamaru, a lokacin da Boko Haram suka kawo wata wawar kora.