Shirin Rage Talauci Na NSIP: Shugaba Buhari Yayi Kokari, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Dama ita gwamnati kowacce iri ce, ana iya gane ingancinta idan tana iya samar da abubuwan da zasu canza rayuwar talakawa.

Talauci babban barazana ne ga rayuwar dan Adam, kuma ko ina akwai talaka duk duniya, ya danganta da yadda gwamnati take kokari wajen samar da yanayi mai kyau wanda zai bawa talakawa damar kubuta daga talauci.

Shirin ‘Social Investment Programmes” wanda ya hada da Npower, Cash Transfer, School Children Feeding, Geep Loan, Trader Moni da sauransu, sun bayyana tasirinsu a rayuwar talakawan Najeriya.

Shirin Npower ya samar wa da matasa dubu dari biyar aikin wucin-gadi, wadannan matasan suna kar6ar dubu talatin (30k) duk wata, yin hakan ya rage zafin talauci da rashin aikin yi a Najeriya.

Shirin Cash Transfer yana da tasirin gaske wajen tsamo mutanen karkara daga halin rashi, musamman mata wadanda suke zaune babu cas babu as. Tabbas shirin yana farantawa mutanen karkara wadanda duke buqatar tallafi.

Cash Transfer wanda ake masa kirari da “Better don com” (Alheri yazo), tsari ne da yake bawa mutanen da suke cikin halin rashi dubu goma (10k) a duk bayan wata biyu, sannan akan wannan tsarin ne ake koyawa wadanda suke cikin tsarin yadda zasu yi sana’a kafin a yayesu. Tabbas naga tasirin tsarin a kauyukan Kano da sauran jihohin kasarmu.

Sannan shirin ciyar da yara ‘yan makaranta (School Children Feeding) yana inganta ilimi a fadin Najeriya, saboda iyaye sun samu sauki da karsashin tura yaransu makaranta tunda gwamnati ta dauki nauyin ciyar musu dasu.

Hakazalika, tsarin Geep Loan da Trader Moni suna bayyana tasirin gwamnati a rayuwar talaka, kamar yadda ‘yan Najeriya suke gani suna faruwa a zahiri a cikin kasarsu.

Irin wadannan abubuwan ne suke bayyana kyawun gwamnati, kuma sune kasashen da suka cigaba suke yi don inganta tattalin arzikin ‘yan kasa a karkashin tsarin “Social Security Administration.”

A kwana a tashi, cikin ikon Allah sai gasu a cikin kasarmu suna faruwa, don bincike ya bayyana yadda shirin ya canza rayuwar da yawa daga cikin talakawan Najeriya. Muna sa rai zasu dore da ikon Allah.

Allah ya shiryar damu.

Share.

game da Author