BOKO HARAM: Gwamnan Barno ya dauki malamai 30 domin yin addu’o’i da dawafi

0

Gwamnan Jihar Barno ya dauki hayar wasu zaratan malamai mazauna kasar Saidiyya 30, domin yin zamar-dirshan a Ka’aba, a Makkah, su na yin addu’o’i da dawafin neman Allah ya kawo karshen Boko Haram.

Wannan lamari ya zo daidai lokacin da Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai, ya nemi a hada da yin addu’a domin kakkabe Boko Haram.

Kakakin Yada Labarai na gwamnan, Abdullahi Bego, ya ce dukkan wadanda aka dauka yin addu’o’in, ba Larabawa na ne, ‘yan Najeriya ne da suka dade a Makkah a zaune can.

“Akwai ‘yan Jihar Barno, Katsina, Zamfara, Kano da wasu jihohi. Kuma duk mazauna cikin birnin Makkah ne. Za su rika shafe lokaci a Ka’aba su na addu’a da yin dawafin neman zaman lafiya. Akwai daga cikin su wani dattijon malami da ya shafe shekaru 40 ya na zaune can ya na ibada.” Inji Bego.

Gwamman wanda a cikin makon da ya wuce sai da ya je har Makkah, inda ya hadu da malaman su 30 a Ka’aba, ya gode musu. Kuma ya ce za a hada da addu’o’i da kuma karfafa matakan tsaro.

Share.

game da Author