Hukumar kula da karatun digiri mai zurfi a kiwon lafiya ta kasa ta bayyana cewa abin tashin hankali ganin yadda likitocin kasar nan da dama ke ficewa zuwa kasashen waje domin samun aikin yi.
Shugaban hukumar Da Lilly-Tariah ya koka a kan haka ne da yake bayani a taron wanke sabbin likitoci 477 da za su sami horon digiri mai zurfi a hukumar da aka yi a Abuja ranar Alhamis.
Da Lilly-Tariah ya bayyana cewa hukumar na fama da matsalar rashin isassun wuraren horas da sabbin likitoci da kuma karancin kudade da hukumar ke fama da shi.
Ya ce wannan matsalar da hukumar ke fama da su na daga cikin matsalolin da ke sa suna kaucewa kasashen waje.
A karshe shugaban kingiyar likitocin Najeriya (NMA) Francis Faduyile kira ya yi ga sabbin likitocin da su rika hakuri suna zama a kasa Najeriya.