Gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello yayi wa masu garkuwa da mutane 13 afuwa dake tsare a kurkukun jihar.
Gwamna Bello ya bayyana haka ne a taron kwamitin zaman Lafiya wanda tsohon shugaban kasa Abdussalami Abubakar yake shugabanta da aka yi a garin Minna.
A wajen taron, gwamna Bello ya ce gwamnati ta zauna da wadannan yan bindiga inda ta suka amince a tsakaninsu cewa zasu daina akata fashi da makami da kuma gaekuwa da mutane.
Su dai wadannan masu garkuwa suna tabargazarsu ne a yankin Kontonkoro dake karamar hukumar Magama.
Gwamna Bello yace gwamnati za ta ci gaba da tattaunawa da mahara a wasu yankunan jihar da ya hada da Pandogari,Allawa da Erena domin ganin an kawo karshen ta’addanci, Hare-hare da garkuwa da mutane a jihar.
Discussion about this post