Manchester City ta yi wa Watford luguden gwalagwalai, Barcelona ta sha kashi

0

A wasan gwallon kafa na Premier league da aka buga ranar Asabar, kungiyar Manchester City ta yi wa Watford luguden gwalagwalai har takwas babu ko daya.

Ita ko Barcelona a can kasar Spain kashin ta ta kwasa a hannu a wajen Granada.

Granada ta lallasa Barcelona da ci 2 babu ko daya.

Duk da cewa shahararren dan watan sa Leo Messi na cikin wannan wasa, wankin hula ya kai Barcelona dare.

Wannan nasara da Granada ta samu ya sa ta dare na daya a Teburin lik din kasar Spain.

Real Madrid za ta buga da Sevilla ranar Lahadi.

Share.

game da Author