An kirkiro katin cirar kudi na ‘ATM’ domin cirar kudi a saukake da kuma aika kudade ta hanyar yin amfani da shi kai tsaye ko a ina ne.
To haka kuma ‘yan damfara ke kara kamari ta hanyar shigo da dabarun satar kudaden mai tsautsayi.
Hukumar Kididdigar Bayanai ta Kasa (NBC), ta bayyana cewa a cikin watanni hudun karshe na shekarar 2018, an yi hada-hadar cira da aika kudade kudade ta hanyar amfani da katin ‘ATM’ har naira tiriliyan 39.15 a fadin kasar nan.
NBC ta ce an tura katin ATM sau milyan 616, 528, 697 a wadannan watanni hudun da aka yi tasarifin naira tiriliyan 39.15.
Duk da cewa jama’a sun amince kuma sun gaskata ATM, akwai masu damfara na shigo da hanyoyin kokarin satar bayanan katin ‘ATM’ ta intanet.
Idan ka sake suka saci bayanan da ke cikin katin ka na ATM, to sai dai ka ji a salansa.
MATAKAN HANA ’YAN DAMFARA SATAR BAYANAN ‘ATM’ DIN KA
Ka yi hankali idan za ka yi amfani da katin ka na ‘ATM’ ta hada-hadar intanet.
Jama’a da dama na sayen kayayyaki ta intanet kai-tsaye. To ka kwana da sanin cewa, kafin ka danna lambar karshe da nufin amincewa a ciri kudin ka, to ka tabbatar cewa shafin intanet din da ka ke mu’amala da su din, gangariya ne ba na bogi ba ne.
Gaskiyar magana dai idan ka na tababar shafin yanar gizo din, to kada ka kuskura ka saki linzamin makullin ‘ATM’ din ka. Yanzun nan sai a bar ka kana susar keya. To idan ka rig aka sayi biri a sama, ya za ka yi?
KA YI AMFANI DA NA’URAR CIRAR KUDI DA AKA KAFA A BANKI
An wayi gari a yanzu ko a jikin wane gini inda ake hada-hada, sai ka ga an kafa na’urar cirar kudi ta hanyar katin ‘ATM’, ga su nan birjik, kamar famfon tuka-tuka. Shawara gare ka ita ce, idan za ka ciri kudi ko za ka tura kudi, to ka je inda aka kafa wannan na’ura ta ‘ATM’ a cikin banki ko a wajen banki. Hanyar lafiya dai inji Hausawa, wai a bi ta a shekara.
Idan za ka yi amfani da katin ka na ATM, to ka rika yin kaffa-kaffa da kayan ka. Ka kula da kayan ka, kuma ka yi masa rikon laya a hannun dan dambe, wato mutu-ka-raba. Idan ka yi sako-sako, za a bar ka kana ’yan kyifce-kyifce!
KA RIKA DUBA BAYANAN SHIGA KO FITAR KUDI DAGA ASUSUN KA
Duk irin kaffa-kaffar da z aka yi da katin ka na ATM da lambobi sirri na ‘PIN’, to duk da haka dai ka rika bincikar bayanan shiga ko fitar kudade daga asusun ka na banki.
Idan ba ka yi aune ba, wata rana sai ka duba, ka ga ashe babu komai a cikin asusun na ka na banki, sai karfanfana kawai.
Da ka ga wani biri-birin bayanan da ba ka gamsu da sahihancin su a cikin asusun ka ba, to ka garzaya bankin ka ka kai rahoto. Ko kuma ka kira su da wayar ka, ko ka tura musu sakon kar-ta-kwana.
Idan kunne ya ji, aljihu ya tsira!