Ba ni na dirka wa Tboss cikin-shege ba –Dino Melaye

0

Sanata Dino Melaye ya musanta zargin da ake yi masa cewa shi ne ya dirka wa Tboss cikin-shege.

Melaye ya karyata wannan zargin ne a Lahadi, dangane da rade-radin da ake yi cewa shi ya yi wa Tboss, wadda ta taba shiga gasar dandalin zaman dirshan na ‘Big Brother Naija housemate’ a 2017 ba.

Melaye, wanda ya taba dirka wa fitacciyar jarumar fina-finan Yarabawa mai suna Bisi Ibidapo ciki, shekaru bakwai da suka gabata, har ta haihu, ya ce bai taba yin lalata da Tboss ba, ko sau daya.

Dino ya shiga shafin sa na Twitter, ya na cewa: “Bai kamata na yi shiru na kyale wasu karairayi na ta yawo ba, wai ni na yi wa Tboss ciki. To kowane jinjiri dai albarka ne ga mahaifiyar sa. Amma fa idan ana neman uban sa, to ba ni ba ne. Ban taba yin lalata da Tboss ba.”

Duk da cewa Tboss wadda cikakken sunan ta Tokumbo Idowo, ta haihu ba tare da mijin aure ba kwanan nan, har yau ta yi shiru ba ta fadi sunan wanda ya dirka mata ciki ba.

Dalilin haka ne ‘yan fim da dama da arakashe irin su Ubi Franklin, Uti Uwachukwu da Senator Dino Melaye duk ake radi-radin cewa cikin na su ne.

Sai dai kuma ita Tboss ta ce ba ta taba yin lalata da ko daya daga cikin su ukun ba.

Share.

game da Author