RANAR ‘YANCI: Kada mazauna Abuja su rude idan sun ji rugugin bindigogi -Sojoji

0

Rundunar Sojojin Najeriya ta fitar da sanarwar kada mazauna Abuja su firgita idan su ka ji karar harbin bindigogi na nashi a ranar 1 Ga Oktoba.

Wannan rana ce dai Najeriya ke cika shekaru 59 da samun ‘yanci. Kuma an shirya sojoji za su yi wa Shugaba Muhammadu Buhari faretin ban-girma a cikin Fadar Shugaban Kasa a ranar.

Faretin wanda sojojin Guards Brigade za su yi, an yi kira ga musamman mazauna unguwannin Asokoro, Maitama da kewayen Fadar Shugaban Kasa, idan sun ji karar rugugin tashin bindigogin ‘Artillery’, kada su razana, su kwantar da hankalin su.

Mataimakin Kakakin Yada Labarai na Sojojin, Haruna Tagwai ne ya fitar da sanarwar, kuma shi ne ya sa mata hannu.

“Za a harba bindigogin ‘artillery’, kuma kada mutane su firgita, musamman mazauna Maitama, Asokoro da kewaye.”

Gwamnatin Buhari dai ta ce ta ware ranar I Ga Oktoba ta ci gaba da zama ranar murnar samun ‘yanci. Yayin da ta kebe ranar 12 Ga Yuni ta zama Ranar Dimokradiyya, domin karrama marigayi MKO Abiola, wanda aka soke zaben da ake gani shi ne ya yi nasara da aka gudanar a ranar 12 Ga Yuni, lokacin mulkin Ibrahim Babangida.

Share.

game da Author